Mutanen Gari Sun Kama 'Yan Bindiga Hannu da Hannu, Sun Kashe Su har Lahira

Mutanen Gari Sun Kama 'Yan Bindiga Hannu da Hannu, Sun Kashe Su har Lahira

  • Rahotanni na nuni da cewa 'yan bindigar da suka kai hari yankin Tafoki a Faskari, Katsina sun gamu da fushin jami’an tsaro
  • A yayin musayar wuta, wasu daga cikin ’yan bindigar sun samu munanan raunuka kuma suka tsere zuwa daji da suka sha wuta
  • An ruwaito cewa washegari, mazauna garin sun kama wasu daga cikin raunanan ’yan bindigar su uku kuma suka kashe su nan take

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Mazauna kauyen Tafoki da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina sun hallaka ’yan bindiga uku da suka jikkata a lokacin da suka kai hari da ya ci tura.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu, ’yan bindiga dauke da manyan makamai suka dirar wa Tafoki a kan babura kusan 100.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ɓullo da sabuwar dabara, mataimakin ciyaman ya faɗa tarko a Zamfara

Yan bindiga
Mutanen gari sun kashe 'yan bindiga a Katsina. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ne ya bayyana yadda mutanen garin suka kama 'yan ta'addan kwana daya da kai harin a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa jami’an tsaro tare da hadin gwiwar matasan yankin sun yi gaggawar mayar da martani yayin da 'yan ta'addan suka kai hari garin.

Martanin ya tilasta wa ’yan bindigar tserewa bayan sun samu raunuka da dama wanda hakan na cikin dalilan kama wasu daga cikinsu.

Mazauna Tafoki sun yi ramuwar gayya

Bayan harin da ya ci tura, wasu daga cikin raunannun ’yan bindigar sun arce zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu.

Sai dai washegari da safe, wasu mazauna garin Tafoki sun gano ’yan bindiga uku da suka ji raunuka a cikin daji, suka kama su, suka kashe su.

Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan da jama’a suka fusata da yadda ’yan bindiga ke addabar su, musamman bayan harin da aka kai musu a baya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai wa fulani makiyaya hari, an sace basarake da wasu mutum 38

Wasu na ganin matakin da mazauna kauyen suka dauka ya dace yayin da wasu ke ganin ya kamata su mika su ga jami'an tsaro domin bincike.

Jami’an tsaro sun dauki mataki

Bayan faruwar lamarin, hukumomin tsaro sun samu rahoton kisan ’yan bindigar kuma ana ci gaba da kokarin kamo sauran da suka gudu.

Rundunar ’yan sanda ta jihar Katsina ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce jami’anta sun bazama domin ganin an dakile barazanar da ke tattare da sauran ’yan bindigar da suka tsere.

Ana ci gaba da daukar matakan tsaro a yankin, tare da hadin gwiwar jami’an tsaro da ’yan banga domin tabbatar da zaman lafiya a Tafoki da kewaye.

A yanzu haka dai ana sa rai ko jami'an tsaro za su kamo sauran 'yan bindigar lura da cewa sun samu raunuka kafin su tsere zuwa cikin daji.

An fatattaki 'yan bindiga a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an tsaron hadin gwiwa sun gwabza fada da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

An budewa sarki wuta da bindiga bayan sace shi a Kaduna, an yasar da gawarsa

Rahotanni sun nuna cewa an gwabza fadan ne bayan 'yan bindigar sun tare wata hanya da niyyar satar mutane da fashi da makami.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng