Daga karshe Shugaba Tinubu Ya Fadi Kudaden da Ake Ba Gwamnonin Najeriya

Daga karshe Shugaba Tinubu Ya Fadi Kudaden da Ake Ba Gwamnonin Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta kamo hanyar durƙushewa da gwamnatinsa ta gaza cire tallafin man fetur
  • Mai girma Bola Tinubu ya ce gwamnonin jihohi za su iya tabbatar da cewa kuɗaɗen da ake ba su yau sun ninka sau uku
  • Shugaban ƙasa ya kuma bayyana cewa cire tallafin man fetur ya taimaka wajen samar da ƙarin kuɗaɗe ga ƙananan hukumomi
  • A sakamakon soke wannan tsari ne gwamnatin tarayya ta samar da bashi ga ɗalibai masu son yin karatun gaba da sakandare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi magana kan kuɗaɗen da ake ba gwamnonin jihohin Najeriya duk wata.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa gwamnonin jihohi za su iya tabbatar da cewa suna samun ƙarin kuɗaɗe don gudanar da ayyukan jihohinsu tun bayan cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya fusata kan yankewa ma'aikata albashi, ya dauki mataki

Tinubu ya fadi abin da gwamnoni ke samu
Tinubu ya fadi kudaden da ake ba gwamnoni Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Wani mai amfani da shafin X, Imran Muhammad ya sanya bidiyon jawabin shugaban ƙasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya halarci taron APC

Shugaba Tinubu ya yi jawabin ne a yayin taron farko na manyan ƙusoshin jam’iyyar APC na ƙasa a birnin tarayya Abuja a ranar Talata, 25 ga watan Fabrairun 2025.

Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa cire tallafin man fetur, shi ne hanyar da za a ceto Najeriya daga halin taɓarɓarewar tattalin arziƙi da ta tsinci kanta a ciki.

Tinubu ya ce babu wata hanya da Najeriya za ta iya tsira daga matsalar tattalin arziƙi da take ciki, idan har bai cire tallafin man fetur ba tun ranar farko da ya hau kan mulki.

Har ila yau, ya ce yana da tabbacin cewa gwamnonin jihohi suna samun ƙarin kuɗaɗe fiye da yadda suke samu a baya.

Tinubu ya yi bayani kan cire tallafin man fetur

Shugaban ƙasan ya ce cire tallafin man fetur ya taimaka wajen samar da wadatattun kuɗaɗe ga gwamnati.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan saukar farashin abinci, ya yi alkawarin karin sauki

Ya ce kuɗaɗen ana amfani da su don gudanar da ƙananan hukumomi da kuma asusun ba da rance ga ɗaliban Najeriya (NELFUND), domin tallafa musu a fannin ilimi.

Tinubu ya ce gwamnati tana iya tsara kyakkyawar makoma ga Najeriya, kuma yana jin daɗin abubuwan da ke faruwa a duniya saboda yana koyar da darasin cewa Najeriya na iya gina kanta tare da taimakawa ci gaban Afirka.

"Babu wata hanya da Najeriya za ta iya cigaba da wanzuwa idan har tallafin man fetur ya ci gaba. Babu wannan hanyar."
"A yau, zan iya bugun ƙirji na kan cewa kowanne gwamna a nan ya san cewa kuɗin da ake bai wa jihohi sun ninka sau uku."

- Shugaba Bola Tinubu

Talaka bai gani a ƙasa ba

Abubakar Mika ya bayyana cewa har yanzu ƴan Najeriya na jin raɗaɗin cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.

Ya bayyana cewa cire tallafin ya ƙara jefa mutane cikin wahala da ƙunci mai tsanani.

Kara karanta wannan

A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC

"Ana maganar gwamnoni sun ƙara samun kuɗaɗe, ko ya hakan zai amfani talaka wanda yake ji a jikinsa kan cire tallafin da aka yi?"
"Ya kamata dai a sake tunani domin mutane na cikin wani hali."

Hadimin Tinubu ya faɗi amfanin cire tallafin mai

A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin shugaban ƙasa kan hulɗa da jama'a, Abdullahi Tanko Yakasai, ya yi magana kan cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.

Abdullahi Tanko Yakasai ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun samu sauƙi sosai sakamakon matakin da gwamnati ta ɗauka na cire tallafin da ta ke biya kan man fetur.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel