Akpabio: Shugaban Majalisa Ya Shiga Matsala bayan Sanata Ta Maka Shi Kara a Kotu

Akpabio: Shugaban Majalisa Ya Shiga Matsala bayan Sanata Ta Maka Shi Kara a Kotu

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ɗauki matakin garzayawa zuwa kotu kan taƙaddamar da take yi da Godswill Akpabio
  • Natasha da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta kai shugaban majalisar dattawan ƙara a gaban babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja
  • Sanatan ta shigar da ƙarar ne bisa zargin ɓata mata suna, inɗa ta buƙaci shugaban majalisar dattawan ya biya diyyar N100.3bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shigar da kara a kotu kan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da Godswill Akpabio ƙara ne bisa zargin ɓata mata suna.

Sanata Natasha ta shigar da Akpabio kara
Sanata Natasha ta kai.Akpabio kara a gaban kotu Hoto: The Nigerian Senate, Natasha H. Akpoti
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa Sanata Natasha ta shigar da ƙarar ne a ranar Talata, 25 ga watan Fabrairun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Natasha ta yi cece-kuce da shugaban majalisa

Kara karanta wannan

"Ku canza tunani," Akume ya ba Atiku, El Rufai da Gwamna Bala shawara kan takara a 2027

A kwanakin baya dai Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta nuna damuwa bayan an sake rabon kujerun zama a majalisa, inda aka mayar da ita wani wuri na daban sakamakon sauya sheƙa da wasu ƴan adawa suka yi zuwa jam’iyya mai mulki.

Sanatan ta nuna rashin amincewa da wannan mataki, wanda hakan ya jawo taƙaddama tsakaninta da shugaban majalisar dattawa.

Natasha ta kai Akpabio ƙara a kotun tarayya

Sai dai, a cikin ƙarar da aka shigar a babbar kotun tarayya da ke Abuja, Natasha ta sanya Akpabio da babban mai taimaka masa kan harkokin majalisa, Mfon Patrick, a matsayin waɗanda ake ƙara, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

A cikin ƙarar mai lamba CV/737/25, lauya mai kare Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Victor Giwa, ya zargi shugaban majalisar da furta maganganun ɓatanci da kuma wallafa su ta hannun mai taimaka masa a shafin Facebook.

A cewarsa, wani rubutun da hadimin na Akpabio ya yi, ya ƙunshi kalaman da ke nuni da cewa Natasha Akpoti-Uduaghan tana tunanin aikin majalisa bai wuce “shan kwalliya da sanya tufafin da za su bayyana jikinta a zauren majalisa” ba.

Kara karanta wannan

"Akwai sauran rigima": Kotu ta yi hukunci kan batun tsige ɗan Majalisar Zamfara

Lauyan ya bayyana cewa waɗannan kalamai na ɓata suna ne, tunzura jama’a, da kuma rage ƙimar mai shigar da ƙarar a idon ƴan majalisa da al’umma baki ɗaya.

Wace buƙata Sanatar ta nema a kotu?

Don haka, Sanatar ta buƙaci kotu da ta hana waɗanda ake ƙara da duk wani mai nasaba da su daga ci gaba da faɗin wasu ƙarin kalaman batanci a kanta, a kowanne dandali.

Bugu da ƙari, Natasha Akpoti-Uduaghan ta buƙaci kotu da ta umarci waɗanda ake ƙara su biya ta Naira biliyan 100 a matsayin diyya da kuma Naira miliyan 300 don biyan kuɗin shari’a.

A cewar takardar ƙarar, sanatan ta roki kotu da ta bayar da umarnin:

"Biyan Naira biliyan 100 a matsayin diyya da biyan Naira miliyan 300 a matsayin kuɗin da shari’a."

Akpabio ya caccaki ƴan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya koka kan halayyar ƴan Najeriya ta rashin son biyan haraji.

Kara karanta wannan

Dakatar da ƴan Majalisa 4 a Kano ya tayar da ƙura, sun yi wa Kwankwaso rubdugu

Akpabio ya bayyana mafi yawancin ƴan Najeriya ba su son biyan kuɗin haraji, amma suna son gwamnatin ta aiwatar da ayyukan ci gaba a ƙasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng