Kashim Shettima Ya Yi Kira ga 'Yan Najeriya bayan Hirar El Rufa'i

Kashim Shettima Ya Yi Kira ga 'Yan Najeriya bayan Hirar El Rufa'i

  • Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bukaci ‘yan Najeriya su rungumi darasin da ke cikin sabon taken ƙasa
  • Kashim Shettima ya bayyana cewa taken Najeriya yana ƙunshe da ƙa’idojin kishin ƙasa da ya kamata kowa ya bi
  • Shettima ya yi magana ne yayin ƙaddamar da wani littafi a Abuja da ya bayyana ma’anonin da ke cikin sabon taken Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bukaci ‘yan Najeriya da su fahimci darasin da ke cikin sabon taken ƙasa tare da amfani da shi a rayuwarsu ta yau da kullum.

Ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da wani littafi mai suna In Brotherhood We Stand a Abuja, wanda ke bayani kan ma’anar sabon taken Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shigo da motocin noma domin yaki da yunwa da samar da abinci

Shettima
Kashim Shettima ya bukaci a nuna kishin kasa. Hoto: Aso Villa
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Shettima, wanda hadiminsa, Dr Aliyu Umar ya wakilta, ya bayyana taken Najeriya a matsayin jagoran kishin ƙasa ga kowane ɗan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Magana kan littafin da aka kaddamar

Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai, Julius Ihonvbere ya ce littafin ba kawai kalmomi ne a takarda ba, yana ƙunshe da tunatarwa kan Najeriya a matsayin ƙasa.

Pulse Nigeria ta wallafa cewa Julius Ihonvbere ya ce:

“Na karanta littafin da kaina, kuma zan iya shaida cewa yana ƙarfafa kishin ƙasa, haɗin kai, da kuma nuna muhimmanci wajen yin hidima ga al’umma.”

Shi ma Shugaban Kamfanin C G, Mike Duru Ejiogu, ya bayyana littafin a matsayin tunatarwa kan asalin Najeriya – watau haɗin kai duk da bambance-bambancen yankuna.

Ya ce littafin ya yi bayani kan wasu manyan ƙa’idojin rayuwa da idan aka bi su za su taimaka wajen gina ƙasar da kowa zai yi alfahari da ita.

Kara karanta wannan

Mubarak Bala da ƴan Arewa 4 da aka taɓa yankewa hukuncin kisa kan ɓatanci ga Annabi

Matan shugabanni sun goyi bayan littafin

Uwargidar Shugaban Kasa, Senata Oluremi Tinubu, wacce ta samu wakilcin Hajiya Fatima Abbas, Uwargidan Kakakin Majalisar Wakilai, ta yaba da littafin.

Hajiya Fatima Abbas ta ce:

“Kalmomin da ke cikin sabon taken ƙasa sun ƙunshi haɗin kai, zaman lafiya da cigaba.
"Taken Najeriya ba wai waƙa ba ne kawai, illa dai cikakken bayani kan tarihin Najeriya, ƙalubalenta, da abi da take son cimmawa a matsayin kasa.”

Shi ma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Senata George Akume, wanda aka wakilta, ya ce littafin zai cike gibin da ke tsakanin ‘yan Najeriya wajen fahimtar ma'anar taken ƙasa.

Ya bada shawarar cewa a rarraba littafin ga matasa da masu riƙe da madafun iko don ƙarfafa kishin ƙasa.

Kira domin nuna kishin kasa

Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, wanda aka wakilta, ya ce fahimtar sabon taken ƙasa ita ce hanya mafi dacewa don farfaɗo da Najeriya.

Kara karanta wannan

"Sai Atiku," Ana tunanin matsalolin Najeriya sun fi karfin gwamnatin Tinubu

Abbas
Shugaban majalisar wakilan Najeriya. Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Twitter

A nasa jawabin, marubucin littafin, Ambasada Osere Daniels, ya bayyana cewa littafin nasa wani ƙoƙari ne na dawo da darajar kishin ƙasa da ɗabi’ar gaskiya a Najeriya.

Shettima ya yi maganar talauci a Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya ce yankin Arewa maso Gabas na fama da talauci sosai.

Kashim Shettima ya yi bayani ne yayin wani taron Arewa maso Gabas domin habaka harkokin zuba jari da farfado da tattalin arziki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng