Zamfara: Mummunar Gobara Ta Lakume Kayan Miliyoyin Naira a Fitacciyar Kasuwa
- Ƴan kasuwa da dama sun shiga jimami bayan an samu tashin mummunar gobara a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma
- Gobarar wacce ta tashi a babbar kasuwar Gusau ta laƙume shaguna masu tarin yawa a daren ranar Lahadi
- Wasu majiyoyi sun bayyana cewa gobarar wacce ta ɗauki sa'o'i tana ci, ta tashi ne bayan an dawo da wutar lantarki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - An samu tashin mummunar gobara a wata fitacciyar kasuwa da ke jihar Zamfara.
Aƙalla shaguna 103 ne suka ƙone ƙurmus a wata gobara da ta tashi a sashen kayan abinci na babbar kasuwar Gusau da ke jihar Zamfara.

Asali: Original
Jaridar Daily Trust ta ce wani daga cikin ma’aikatan kashe gobara ya danganta lamarin da matsalar wutar lantarki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda gobara ta yi ɓarna a Zamfara
Ma'aikacin ya bayyana cewa gobarar ta fara ne jim kaɗan bayan an dawo da wutar lantarki a kasuwar.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare a ranar Lahadi, inda ta ci gaba da ruruwa na tsawon sa’o’i kafin jami’an kashe gobara na tarayya da na jihar Zamfara su kashe ta da misalin ƙarfe 2:00 na dare.
Shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar kayan abinci, Alhaji Inusa Saminu, ya bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki.
"Muna da tabbacin cewa shaguna 103 sun ƙone gaba ɗaya. Ba za mu iya tantance asarar da muka tafka ba a yanzu, amma ta kai ta miliyoyin naira. Akwai manyan kantuna da ke ɗauke da kaya busassu da suka ƙone kurmus."
- Alhaji Inusa Saminu
Ya danganta ɓarnar da gobarar ta yi da jinkirin da jami'an kashe gobara suka yi na kawo agajin gaggawa.
"Muna kusa da wani ofishin masu kashe gobara, amma lokacin da muka kira su, sai suka ce mota ɗaya tilo da suke da ita ta lalace tun watanni da suka gabata."
"Ban fahimci amfanin gina ofishin kashe gobara a kasuwa ba idan har ba za a samar da motoci da kuma kayan aiki masu inganci ba."
"Hatta ofishin hedikwatarsu sun ce babu batir a motarsu lokacin da aka kira su. Dole sai da suka aro batir kafin su iya zuwa, kuma sawu ɗaya kawai suka yi saboda motar ta lalace a hanya."
"Muna roƙon gwamnatin jiha da ta samar da motocin kashe gobara da kuma kayan aiki domin wannan ita ce gobara ta shida da aka samu a kasuwanni a jihar nan, kuma duka sun jawo gagarumar aasara."
- Alhaji Inusa Saminu
Ƴan kasuwa sun buƙaci tallafi
Ya kuma roƙi gwamnati da ta tallafawa ƴan kasuwan da suka rasa dukiyoyinsu a gobarar.
Wani daga cikin waɗanda abin ya shafa, Malam Tanimu, ya tabbatar da cewa kayayyakin da suka kai miliyoyin naira sun salwanta a kasuwar.
“Ina da masaniyar kantuna huɗu da ke dauke da buhunan shinkafa da kayan abinci waɗanda suka ƙone gaba ɗaya."
"Ina tunanin ta yadda za mu farfaɗo daga wannan asara. Ina da tabbacin cewa da dama daga cikinmu ba za su iya komawa kasuwa ba."
- Wani ɗan kasuwa
Gobara ta ƙona ofishin INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mummunar gobara ta laƙume ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta da ke jihar Sokoto.
Gobarar ta tashi ne a ofishin hukumar INEC na ƙaramar hukumar Gwadabawa inda ta lalata kusan dukkanin kayayyakin da aka ajiye.
Gobarar ta tashi ne a ofishin hukumar INEC na ƙaramar hukumar Gwadabawa inda ta lalata kusan dukkanin kayayyakin da aka ajiye..
Asali: Legit.ng