El Rufa'i Ya Yi Martani Mako 1 bayan Tinubu Ya Taya Shi Murna, Ya ba da Hakuri

El Rufa'i Ya Yi Martani Mako 1 bayan Tinubu Ya Taya Shi Murna, Ya ba da Hakuri

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya gode wa masoyansa da suka taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta 65
  • Nasir El-Rufa'i ya ce sakonnin da aka tura masa sun yi matukar yawan gaske har ya gagara mayar da martani ga jama'a
  • Tsohon gwamnan Kaduna ya yi addu’ar Allah ya kara wa kowa lafiya da tsawon rai a fadin Najeriya, kasa mai albarka
  • El-Rufa'i ya ragargaji wasu 'yan siyasa da cewa ba su da niyyar taya shi murna har sai da shugaba Bola Tinubu ya aika masa da sako

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya gode wa masoya, abokai da ‘yan uwa da suka taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta 65.

Kara karanta wannan

"Ba laifin Majalisa ba ne," El Rufai ya fallasa abin da ya sa aka fasa naɗa shi minista

El-Rufa’i ya bayyana cewa sakonnin da aka tura masa sun yi matukar yawa, kuma ya gagara amsawa ko gode wa kowa da kowa.

El Rufa'i
El Rufa'i ya yi martani mako daya bayan taya shi murnar ranar haihuwa. Hoto: Bayo Onanuga|Nasir El-Rufa'i
Asali: Twitter

Legit ta tattaro bayanan da El-Rufa'i ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasir El-Rufa’i ya gode wa masoyansa

A cikin sakon da ya wallafa, El-Rufa’i ya ce ya yi kokarin mayar da martani ga dukkan sakonnin da aka tura masa, amma ya san cewa ba zai iya amsa wa kowa ba.

Tsohon gwamnan ya ce:

"Na gode wa duk wanda ya tura mani sakon taya murna da addu’o’i.
"Wasu sun yi shiru sai da shugaba Tinubu ya taya ni murna. Allah ya karbi addu’o’inmu, ya kuma ci gaba da sanya albarka a rayuwarmu."

Tsohon gwamnan ya ce Bola Tinubu ya kunyata wadanda suka yi shiru wajen taya shi murnar har sai da fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa sannan suka taya shi.

Kara karanta wannan

El Rufa'i zai yi zazzaga, zai yi hirar farko bayan sauka daga gwamna

El-Rufa'i ya yi addu’a ga Najeriya

El-Rufa’i ya kara da cewa yana addu’ar Allah ya kara wa kowa lafiya da tsawon rai a cikin Najeriya mai cike da albarka da ci gaba.

Ya ce:

"Ina fatan Allah ya kara mana lafiya, tsawon rai, farin ciki da arziki a Najeriya,"

El-Rufa'i ya nemi afuwar jama'a

Tsohon gwamnan ya bukaci gafara daga duk wanda bai amsa masa sakonsa ba, inda ya ce hakan alama ce da idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai.

El-Rufa'i
El-Rufa'i yayin ganawa da wasu 'yan adawa. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Twitter

A cewar El-Rufa'i:

"Na yi kokarin amsa dukkan sakonnin da aka aika min, amma matsayina na mutum mai rauni, ba zan iya tabbatar da cewa na amsa wa kowa ba.
"Idan ban yi martani ga sakon ka ba, don Allah ka yafe mani."

APC da PDP sun raba gari kan El-Rufa'i

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta yi magana kan alamun raba kafa da Nasir El-Rufa'i ke yi a fagen siyasa.

Kara karanta wannan

2027: PDP da APC sun fara cacar baki kan shigar El Rufa'i cikin 'yan adawa

APC ta nuna rashin gamsuwa da hakan yayin da a daya bangaren kuma PDP ta ce kofar ta a bude take wajen ba shi damar shiga cikinta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng