Barau Ya Rikita Kano da Kyautar Motoci da Babura, Ya Yi Alkawari ga Matasa da Malamai
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya raba motoci 61 da babura 1,137 ga shugabannin APC a jihar Kano
- Taron ya gudana ne a wani wajen taro, inda manyan jiga-jigan jam’iyyar APC suka halarta, ciki har da Dr Abdullahi Umar Ganduje
- Sanata Barau ya ce tallafin somin tabi ne, saboda haka zai ci gaba da bai wa matasa, manoma, mata da malamai tallafin kayayyaki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya kaddamar da shirin tallafa wa shugabannin jam’iyyar APC a Kano.
A cewarsa, ya fara ne da rabon motoci 61 da babura 1,137 ga shugabannin jam’iyyar APC a kananan hukumomi 44 da mazabu 484 na jihar.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan rabon kayan ne a cikin wani sako da mataimakin majalisar dattawan ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar da cewa an gudanar da bikin rabon tallafin ne a dakin taron Meena da ke titin Lodge a jihar Kano, inda manyan jiga-jigan APC suka halarta.
Barau ya yi rabon motoci da babura
Daya daga cikin jagororin APC a jihar Kano, Sanata Barau Jibrin ya gwangwaje shugabannin jam'iyya da motoci da babura.
Sanata Barau ya bayyana cewa wannan tallafi wani yunkuri ne na karfafa shugabannin jam’iyyar APC, kasancewar su ne ginshikin ci gaban siyasa a matakin kasa da jiha.
Barau Jibrin ya ce:
"Wannan farkon tafiya ce. Muna da shirin tallafa wa al’ummar Kano gaba ɗaya, ba shugabannin APC kadai ba.
"Za mu ci gaba da rabon kayan tallafi ga matasa, manoma, mata, ‘yan kasuwa da malamai."
Muhimmancin goyon bayan gwamnatin Tinubu
Sanata Barau ya yaba wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa shirye-shiryen da gwamnatinsa ke yi na inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa gwamnatin Tinubu cikakken goyon baya domin ganin an aiwatar da shirye-shiryen raya kasa.
Wasu na ganin rabon kayan na da alaka da shirye shiryen siyasar 2027, musamman lura da cewa Kano na hannun jam'iyyar adawa ta NNPP.
Ganduje da sauran mahalarta taron a Kano
Taron rabon tallafin ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, ciki har da shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Asali: Facebook
Sanata Barau ya jaddada cewa nan gaba zai fadada shirin, inda zai tabbatar da cewa kowane bangare na al’umma ya amfana daga tallafin da yake bayarwa.
Masana siyasa na ganin halartar jiga jigan jam'iyyar APC taron na cikin kara karbuwar Sanata Barau Jibrin a hannun magoya bayan jam'iyyar APC a jihar Kano.
Ministan gidaje ya musa zancen fita a APC
A wani rahoton, kun ji cewa ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Ata ya yi karin haske kan maganar barazanar ficewa daga jam'iyyar APC.
Abdullahi Ata ya ce ba a fahimci maganar da ya yi ba a yayin taron APC, ya ce yana cikin APC kuma zai cigaba da goyon bayan Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng