Ni Ba Ba-Yarbe Bane: IBB Ya Fadi Gaskiyar Karin Sunan ‘Babangida’ a Cikin Sunansa
- Tsohon shugaban Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana yadda ya yi kari kan sunansa domin kaucewar wata matsala
- A bayaninsa cikin littafin da ya wallafa, ya ce akwai wadanda ke masa kallon Ba-Yarbe duk da kasancewarsa dan asalin Arewacin Najeriya
- A littafin ne dai ya bayyana kusan komai da ke da alaka da rayuwarsa kama da yarinta har zuwa aiki da tsufarsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Najeriya - Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya bayyana cewa wasu sojoji sun taɓa zaton shi Ba-Yarbe ne a farkon shekarunsa a aikin soja.
IBB ya ce, dalilin hakan shi ne, suna rikita sunansa na “Badamasi” da sunan Yarbawa “Gbadamosi.”
A cikin littafinsa mai suna A Journey in Service, Babangida ya bayyana cewa wannan rashin fahimta ya sa ya yanke shawarar ƙara sunan mahaifinsa “Babangida” don kauce wa kuskuren fahimta.

Asali: Getty Images
Yadda lamarin ya faru
Babangida ya ce bayan ya dawo daga Indiya a watan Janairu 1964 da matsayin Second Lieutenant, an tura shi zuwa rundunar Reconnaissance Squadron (Turaki Squadron) a ƙarƙashin First Brigade da ke Kaduna.

Kara karanta wannan
"Yadda na hadu da Maria, ta Muslunta muka yi aure, ta koma Maryam," IBB ya ba da labarin soyayyarsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, babban kwamandan First Brigade a wancan lokaci shi ne Birgediya Samuel Adesujo Ademulegun. Sai dai a matsayinsa na matashin jami’i, bai cika samun damar haɗuwa da shi ba.
A kalamansa:
“Muna da manyan jami’ai irinsu Manjo Chris Anuforo, Manjo Hassan Katsina, da Manjo Okpo Isong a matsayin shugabanninmu. Wadannan manyan jami’ai sun nuna min kulawa ta hanyoyi daban-daban.”
Dalilin da yasa ya kara Babangida a sunansa
Duk da haka, kafin ya saba da aiki a Kaduna, wata matsala ta sa shi ƙara sunan mahaifinsa.
Ya ce:
“Lokacin da aka gayyace ni wasu taruka, sojoji da yawa suna rikita sunana, suna ɗauka cewa ‘Badamasi’ wani nau’i ne na ‘Gbadamosi’. Suna tambaya ko ni Ba-Yarbawa ne.”
IBB ya ce wannan ba shi ne karo na farko da aka tambaye shi haka ba. Tun a lokacin da yake shirin shiga aikin soja, an taɓa tambayarsa wannan tambaya.

Asali: Twitter
Ya kara da cewa:
“Sakamakon haka, na yanke shawarar ƙara sunan mahaifina—Babangida—domin a daina samun wannan rudani. A lokacin, na taɓa yin wasa da cewa: ‘Ko da na canza suna, har yanzu dai ni ɗan mahaifina ne!’”
Sabon matashi a soja
Babangida ya bayyana cewa bayan dawowarsa daga Indiya, an sa shi a wani matakin gwaji, kamar yadda ake yi wa sabbin jami’ai da suka yi karatu a ƙasashen waje.
Ya ce an duba ƙwarewarsa da halayyarsa tsawon watanni kafin a yanke shawarar ko zai ci gaba da aiki da cikakken matsayi.
A cewarsa:
“A ƙarshe, bayan wani lokaci, an gama duba cancanta ta. Rahoton ƙarshe ya nuna cewa na cancanta, kuma an ba ni damar ci gaba da aiki.”
Yadda IBB ya gamu da matarsa
A bangare guda na littafin, ya bayyana yadda ya hadu da matarsa Maryam har ta kai ga suka yi aure tare da tara yara.
A bayanansa, y ace ta dalilinsa Maryam ta Muslunta, har da sauya suna daga Maria zuwa sunanta na Maryam da aka sani.
Hakazalika, ya bayyana irin soyayyar da yake mata da kuma yadda suka tsara zamantakewar aurensu zuwa girma.
Asali: Legit.ng