Kungiyar Musulmai Ta Taso IBB a Gaba, Ta Ce Abin Kunya Ne Wasu Magangunan da Ya Yi a Littafinsa

Kungiyar Musulmai Ta Taso IBB a Gaba, Ta Ce Abin Kunya Ne Wasu Magangunan da Ya Yi a Littafinsa

  • MURIC ta bayyana bacin ranta ga yadda IBB ya nuna rashin kulawa da abin da ya faru a zaben da aka yi a shekarar 1993
  • Kungiyar ta nuna damuwa da cewa, sam IBB bai nunawa damuwa ko nadamar soke zaben da aka gudanar a shekarar ba
  • Hakazalika, ta zargi sauran shugabannin Najeriya da Rashin fahimtar abin da ‘yan kasar nan ke bukata, musamman ta fuskar shugabanci

Najeriya - Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) ta zargi tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (rtd), da yunƙurin wanke kansa daga soke zaɓen ranar 12 ga Yuni, 1993.

A wata sanarwa da Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa yayin ƙaddamar da tarihin rayuwarsa, Babangida, wanda aka fi sani da IBB, bai nuna nadama ba, har ma da dora laifin kan wasu.

MURIC ta taso IBB a gaba kan maganganunsa
MURIC ta ce kuskure ne maganganun IBB kan Abiola | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Kalaman MURIC kan tsohon shugaban kasa IBB

A cewar Akintola:

Kara karanta wannan

'Ya zama dole': IBB ya fadi musabbabin kifar da gwamnatin Buhari, ya jero kura kurai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (rtd), wanda aka fi sani da IBB, ya gabatar da tarihin rayuwarsa mai taken 'A Journey In Service' ga jama'a a Transcorp Hilton, Abuja, a ranar Alhamis, 20 ga Fabrairu, 2025.
"Mu a Kungiyar Kare Hakkin Musulmi mun ki yarda da duk wani yunƙuri na tsohon shugaban mulkin soja na wanke kansa daga soke zaɓen ranar 12 ga Yuni, 1993.
“Ya kamata tsohon shugaban ya daina dora laifin kan wasu. Muna bayyanawa a fili cewa alhakin ya rataya a kan IBB. Mun gaza gamsuwa da hujjojinsa."

Dalilin da yasa MURIC ta barranta da batutuwan IBB

Akintola ya bayyana cewa IBB ne ke da alhakin gazawar Najeriya wajen samun tsarin siyasa mai dorewa, hangen nesa, da kuma mutunci, bayan soke zaɓen mafi adalci, sahihanci, kuma mafi lumana a tarihin Najeriya.

Ya ƙara da cewa ranar da IBB ya gabatar da tarihin rayuwarsa ta kasance ranar baƙin ciki ga 'yan Najeriya masu kishin ƙasa na gaske, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

El-Rufai ya sake dagula siyasa, ya gana da shugabannin PDP, an yada hotunan ganawar

“Domin ita ce ranar da shugabannin Najeriya suka yanke ƙaunar talakawa ta hanyar girmama tsohon shugaban mulkin soja, mai mulkin kama karya, kuma babban maƙiyi ga dimokuraɗiyya."
"Najeriya tana dab da faɗawa cikin rami lokacin da Buhari da Idiagbon suka zo don ceto ƙasa daga rashin ɗa'a, cin hanci da rashawa, da kuma ƙazamin kwaɗayi.
“Muna kan hanya madaidaiciya lokacin da IBB ya zo baktatan ya kifar da wannan mulkin gyara. Wannan ne ya zama farkon komawarmu cikin duhu.”

MURIC ta tono batun daure Buhari da IBB ya yi

Da yake karin bayani game da abin da ya faru a wadancan shekarun, Akintola y ace:

"IBB ya tsare Buhari kuma ya hana shi halartar jana'izar mahaifiyarsa. Rayukan 'yan Najeriya masu yawa marasa laifi sun salwanta a lokacin mulkin kama karya na IBB zuwa Abacha. An kashe Clement Akpangbo, Bagauda Kaltho, Justice Ikpeme, Alfred Rewane, da sauransu. Titunan Legas da Ibadan sun cika da gawawwaki."

Kara karanta wannan

Zamfara: Sojoji sun lalata sansanin rikakken dan ta'adda, sun kwashe buhunan abinci

"Amma mafi muni kuma rashin imani shi ne kisan gilla da aka yi wa wanda ya lashe wannan zaɓen mai tarihi, Cif Moshood Kashimawo Abiola (MKO) da kuma kisan matarsa, Hajiya Kudirat Abiola."
MURIC ta caccaki IBB
MURIC kan batun IBB na zaben 1993 | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

MURIC ta yi Allah wadai da mulkin IBB

MURIC ta yi Allah wadai da wannan taron nuna ƙiyayya, ba'a, da rashin tausayi da aka gudanar a Transcorp Hilton, wurin gabatar da littafin na IBB.

A cewarsa:

“Wannan ba kawai rashin kunya ba ne kawai, abin ƙyama ne, abin ki ne a zuciya, kuma abin tayar da hankali. An ƙara wa rauni gishiri. IBB bai nuna nadama ba."

MURIC ta tuhumi shugabannin Najeriya da halin ko in kula

Shugaban MURIC ya bayyana cewa shugabannin Najeriya sun gaza koyon fasahar warkar da raunin al'umma, domin ba su fahimci mutanen da suke jagoranta ba.

Ya bayyana cewa abin takaici ne yadda aka lalata ƙa'idar adalci da addinin Musulunci ya ɗora muhimmanci a kai, ta hannun waɗanda ya kamata su fi kowa sani.

Kungiyar MURIC dai ta kasance daya daga cikin kungiyoyin Najeriya da ke da muryar isar da sako mai zafi ga shugabannin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.