“Yadda Na Hadu da Maria, Ta Muslunta Muka Yi Aure, Ta Koma Maryam,” IBB Ya Ba da Labarin Soyayyarsa

“Yadda Na Hadu da Maria, Ta Muslunta Muka Yi Aure, Ta Koma Maryam,” IBB Ya Ba da Labarin Soyayyarsa

  • Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana yadda ya hadu da matarsa ha rya aure ta
  • Ya bayyana hakan ne a cikin littafin da ya wallafa kwanan nan, inda ya fadi kusan komai game da rayuwarsa da aikinsa
  • Ya kuma shaida irin tasirin da matarsa ke da shi a rayuwarsa da yadda ta kasance mace mai bas hi gudunmawa a kowanne lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Najeriya - Tsohon Shugaban Soja na Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya bayyana yadda ya hadu da matarsa, Marigayiya Maryam Babangida, a cikin littafin na tarihin rayuwarsa mai suna ‘A Journey in Service’.

A littafin, Babangida ya bayyana yadda soyayyarsu ta fara, yadda ya nemi aurenta, da kuma yadda ta karɓi addinin Musulunci kafin su yi aure.

Yadda IBB ya gamu da matarsa Maryam
Tsohon shugaban kasa IBB da matarsa Maryam | Hotuna: Ekpie via Getty Images
Asali: Twitter

Yadda suka hadu

Babangida ya ce ya fara haduwa da Maryam, wadda a lokacin ake kira da Maria Okogwu, a lokacin yana matashin soja.

Kara karanta wannan

Yadda adawar manyan yan siyasar Najeriya za ta shafi tasirin gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wancan lokacin, yana zaune a gidan maza na sojoji a titin Kanta da ke Kaduna, inda yake yawan ganin Maryam saboda dangantakar da ke tsakaninta da abokinsa, Garba Duba.

Ya bayyana Maryam a matsayin kyakkyawar budurwa da take da murmushi mai haskaka fuska da kyau na musamman.

A cewarsa, soyayya ta kullu a tsakaninsu, amma a lokacin yana da takatsantsan saboda girmamawa ga iyayen Maryam.

Babangida ya ce ya taba tafiya don samun wani horon soja a kasashen India da Birtaniya, amma duk da haka, dangantakarsa da Maryam ta ci gaba da wanzuwa.

Yadda ya yanke shawarar aurenta

Babangida ya bayyana cewa ya fara tunanin aure ne yana da shekaru 28, bayan ya samu rauni a filin daga.

A lokacin da yake jinya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas (LUTH), ya fara nazarin irin dangantakar da yake da su da mata daban-daban, amma sunan Maria ne ya fi yawan shigowa ransa.

Kara karanta wannan

Tazarce: Minista ya fadi jihar Arewa da Tinubu zai samu ruwan kuri'u a zaben 2027

A wannan lokaci ne Shugaban Kasa na wancan lokacin, Janar Yakubu Gowon, ya yi aure da matarsa, Victoria, kuma bikin ya kara shajja’a shi da tunanin yin aure.

Matar tsohon shugaban kasa, Maryam Babangida
Hoton matar tsohon shugaban Najeriya, Maryam Babangida | Hoto: Ekpie via Getty Images
Asali: Twitter

Yadda ya yi mata tayin aure

Bayan an sallame shi daga asibiti, Babangida ya wuce Kaduna domin neman auren Maryam. A cewarsa, a farkon tayin auren, Maryam ta nuna shakku game da gaskiyar soyayyarsa saboda sunansa na matashin soja da ke da dangantaka da mata da dama.

Amma daga baya, da taimakon mahaifin Garba Duba, wato Muhammadu King, wanda shi ne kawun Maryam, Babangida ya samu damar shawo kanta ta amince da tayin nasa.

Sauya addini da rayuwar aurensu

Babangida ya bayyana cewa addini yana da muhimmanci a rayuwarsa, kuma ya bukaci Maryam ta karɓi addinin Musulunci kafin su yi aure.

Maryam ta amince da hakan ba tare da wata matsala ba saboda tun asali tana da asali daga gida mai addinin Kirista da Musulunci.

Kara karanta wannan

Matashi ya gayyaci abokinsa gida ya masa kisan wulakanci da adda, ya sassara shi

Bayan aurensu, Maryam ta sauya addini cikin sauƙi kuma ta dace da rayuwa a matsayin musulma.

Babangida ya ce tun kafin aurensu, ya tabbatar mata da cewa ba zai auri mata fiye da ɗaya ba, domin yana son tsayayyen zaman aure da iyali cike da kwanciyar hankali.

Ya ce ya koyi darasi daga wasu sojoji da ma wasu ‘yan uwansa da suke da mata fiye da ɗaya, inda hakan ya janyo musu matsaloli da tashin hankali.

Rayuwarsu bayan aure

IBB da Maryam sun yi aure a ranar 6 ga watan Satumba, shekarar 1969, kuma Allah ya albarkace su da ‘ya’ya huɗu: Aisha, Muhammad, Aminu da Halima.

Babangida ya ce a tsawon rayuwarsu tare, Maryam ta kasance abokiyar rayuwarsa, mai tallafawa burinsa da kuma kwantar masa da hankali a lokutan da yake fama da matsaloli.

Ya bayyana yadda Maryam ta kasance mai kishin rayuwar iyali da tarbiyyar yara, tare da kokarin tallafa wa mata da marasa galihu, wanda hakan ya sa ta kafa gidauniyar Better Life for Rural Women.

Kara karanta wannan

'Ba shi da tsoro ko kadan': Abin da Tinubu ya ce bayan babban rashin da Najeriya ta yi

Tasirin Maryam a rayuwarsa

A cikin littafinsa, Babangida ya bayyana cewa rayuwarsa da Maryam ta kasance cike da soyayya da jituwa, kuma har yanzu yana jin kewarta tun bayan rasuwarta a shekarar 2009.

Ya ce a duk lokacin da ya tuna da lokacin da suka hadu da irin rayuwar da suka yi tare, yana godiya ga Allah da ya ba shi damar kasancewa da Maryam a matsayin matarsa.

Babangida ya kammala da cewa, tarihin rayuwarsa ba zai cika ba ba tare da an ambaci irin rawar da Maryam ta taka a rayuwarsa da kuma gudummawar da ta bayar ga al’umma ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.