Sojoji, 'Yan Sanda da 'Yan Banga Sun Hadu Sun Gwabza Artabu da 'Yan Bindiga
- Rundunar sojojin Najeriya ta ceto mutane 25 da aka yi garkuwa da su a kauyukan Garungabas da Kundu, Rafi, Jihar Neja
- Dakarun sun kwato shanu 22 da tumaki tara da ‘yan bindiga suka sace bayan artabun da sojoji suka yi da su
- A wani hari daban, ‘yan bindiga sun budewa wata mota wuta daga Sokoto zuwa Minna, inda suka kashe fasinjoji biyu tare da jikkata wasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Rundunar sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar jami’an tsaro sun kai samame kan ‘yan bindiga a kauyukan Garungabas da Kundu da ke karamar hukumar Rafi a Jihar Neja.
A cikin harin, dakarun rundunar tsaro sun ceto mutane 25 da aka yi garkuwa da su, tare da kwato shanu 22 da tumaki tara da ‘yan bindiga suka sace daga manoma.

Asali: Facebook
Bayanai da Zagazola Makama ya wallafa a X sun tabbatar da cewa jami’an sojoji, ‘yan sanda da ‘yan banga ne suka aiwatar da wannan sumame domin dakile ayyukan ta’addanci a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka farmaki ‘yan bindiga
Bisa ga bayanan sirri da aka samu, dakarun tsaro sun kaddamar da harin ne a ranar 21 ga watan Fabrairu, 2025, bayan samun labari kan inda ‘yan bindigar suke.
A lokacin samamen, jami’an tsaro sun yi artabu da ‘yan bindigar, inda suka fatattake su, har suka samu damar kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.
Bincike ya nuna cewa mutanen da aka ceto sun hada da maza da mata da aka yi garkuwa da su daga kauyuka daban-daban a yankin.
Bayan ceto tarin mutanen, an kai su sansanin sojoji domin duba lafiyarsu tare da mayar da su ga iyalansu.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi ragargaza mai zafi, sun kashe 'yan ta'adda 82, sun kwato tarin makamai

Asali: Facebook
Sojoji sun kwato dabbobi wajen ‘yan bindiga
Baya ga ceton mutanen, jami’an tsaro sun kwato shanu 22 da tumaki tara da ‘yan bindigar suka sace daga manoma a yankin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yayin samamen, dakarun tsaro sun samu nasarar tarwatsa sansanin ‘yan bindigar, lamarin da ya sa sauran dabbobin da aka sace suka tsere zuwa daji.
Wannan nasara na daga cikin matakan da hukumomi ke dauka domin rage matsalar garkuwa da mutane da satar dabbobi a yankin Neja da sauran jihohin Arewa.
Hukumomi sun bukaci al’umma da su ci gaba da bayar da bayanan sirri domin ci gaba da fatattakar ‘yan ta’adda daga yankin.
'Yan bindiga sun kashe fasinjoji
A wani lamari daban, ‘yan bindiga sun budewa wata motar fasinja wuta a kan hanyar Sokoto zuwa Minna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu.

Kara karanta wannan
'Yan ta'adda na kara karfi, sun kai hari kan jami'an tsaro inda ake zargin Turji ya boye
Bayanai sun nuna cewa ‘yan bindigar sun yi wa mota kirar Sharon kwanton ɓauna a kusa da mafakar su, inda suka fara harbi ba kakkautawa, wanda ya jikkata wasu fasinjoji da dama.
Sojoji sun kashe 'yan bindiga 82
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar tsaron Najeriya ta fitar da rahoton wata-wata kan nasarar da ta samu.
Rahoton rundunar tsaro ya nuna cewa ta kashe 'yan ta'adda kusan 100 tare da kama da dama da kwato tarin makamai a cikin wata daya.
Asali: Legit.ng