Bayan Saukar Abinci, Gwamnatin Tinubu za Ta Karya Farashin Kayan Gini
- Rahotanni na nuni da cewa wamnatin Tarayya za ta kafa cibiyoyin kera kayan gini a shiyyoyi shida na Najeriya
- Manufar shirin shi ne rage dogaro da kayan gini na kasashen waje da kuma bunkasa samar da gidaje masu saukin kudi
- Ana sa ran cibiyoyin za su taimaka wajen samar da ayyukan yi musamman ga matasa da bunkasa tattalin arzikin kasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan Gidaje da Raya Birane, Ahmed Musa Dangiwa, ya ce sabon shirin gwamnati na kafa cibiyoyin kera kayan gini a shiyyoyi shida zai rage farashin kayan gini a Najeriya.
Ahmed Musa Dangiwa ya bayyana haka ne a wani taro da Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane ta shirya tare da masu ruwa da tsaki a fannin gidaje a birnin Legas.

Asali: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa ministan ya ce bunkasa samar da kayan gini a cikin gida zai taimaka wajen rage dogaro da kasashen waje, wanda hakan zai saukaka farashin gidaje ga ‘yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihohin da za a kafa cibiyoyin kayan gini
Minista Ahmed Dangiwa ya bayyana cewa za a kafa wadannan cibiyoyi ne a yankunan da ke da kasuwanni masu girma domin samun saukin kasuwanci da kuma rage matsalolin dokoki.
Ya ce za a kafa cibiyoyin ne a jihohin Abia, Ogun, Kwara, Kano, Gombe da Delta, inda kowace cibiya za ta rika samar da kayan gini ga yankinta.
Dangiwa ya ce matakan rage haraji, tallafi ga masana’antu, da bayar da lamuni mai saukin biya za su taimaka wajen bunkasa fannin gina gidaje.
Ma'aikatar yada labarai ta wallafa cewa ministan ya ce:
“Samar da kayan gini a cikin gida zai taimaka wajen rage dogaro da kayan da ake shigowa da su daga waje.
"Hakan zai taimaka wajen rage farashin gine-gine da kuma samar da damarmakin ayyukan yi.”

Asali: Twitter
Majalisar za ta mara wa shirin baya
Mataimakin Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin Gidaje, Sanata Victor Umeh, ya tabbatar da cewa Majalisa za ta samar da dokoki da manufofi da za su kawo nasarar shirin.
Ya ce Majalisar za ta yi aiki don ganin an rage haraji, an bayar da tallafi ga masana’antun gida, da kuma samar da rance mai sauki ga kamfanonin kera kayan gini.
A cewarsa,
“Wadannan cibiyoyin za su taimaka wajen bunkasa fannin gine-gine da rage radadin matsalar rashin gidaje a Najeriya.
"Za mu tabbatar da an samar da kayayyakin more rayuwa da kuma dokokin da za su saukaka aiwatar da shirin.”
An bukaci karin goyon baya
Babban Sakataren Ma’aikatar Gidaje, Dr Shuaib Belgore, ya ce an yi taron ne domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan hanyoyin bunkasa samar da kayan gini a cikin gida.
Ya ce akwai bukatar inganta dokokin da ke da alaka da wannan fanni, kara hanyoyin samar da wutar lantarki, da kuma inganta hanyoyin sufuri domin rage tsadar kayayyaki.
A cewarsa, wasu muhimman abubuwan da suka kamata a tattauna su sun hada da:
- Inganta dokoki don bunkasa kera kayan gini a cikin gida.
- Rage kudin wutar lantarki domin rage farashin sarrafa kayayyakin gini.
- Samar da rance mai sauki ga masana’antun gini.
- Bunkasa ilimi da horaswa kan fasahar gine-gine.
Ana sa ran wannan shiri zai taimaka wajen rage matsalar rashin gidaje a Najeriya tare da samar da gidaje masu saukin kudi ga ‘yan kasa.
An kafa kwamishinonin haraji 50
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da haraji guda 50 domin lura da harkokin haraji.
Ministan kudi, Wale Edun ya ce kwaminishinonin za su yi aiki a fadin Najeriya tare da samun ofis a jihar Legas da birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng