Kwana Ya Ƙare: Gwamna Ya Kaɗu da tsohon Sanata Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Najeriya

Kwana Ya Ƙare: Gwamna Ya Kaɗu da tsohon Sanata Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Najeriya

  • Tsohon sanatan Ogun ta Yamma, Ayodeji Otegbola ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 91 a duniya
  • Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai, ƴan uwa da abokan arzikin mamacin tare da addu'ar Allah ya ba su haƙuri
  • Abiodun ya bayyana cewa mutuwar sanatan babban rashi ne ga jihar Ogun da ma Najeriya baki ɗaya, ya yi addu'ar Allah ya gafarta masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan tsohon Sanata Ayodeji Otegbola, wanda ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

Marigayi Otegbola, wanda ya wakilci mazaɓar Ogun ta Yamma a zauren majalisar dattawa a Jamhuriya ta uku, ya rasu ne a ranar Litinin da ta gabata.

Gwamna Abiodun.
Gwamna Abiodun ya yi ta'aziyyar rasuwar tsohon sanata a jihar Ogun Hoto: Prince Dr. Dapo Abiodun
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa tuni iyalai da ƴan uwan marigayin suka fara karɓar saƙkonnin gaisuwa daga mutane daban-daban a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Dapo Abiodun ya yi alhinin wannan rashi tare da miƙa sakon ta'iyya ga iyalan mamacin a wata sanarwa da ya fitar.

Gwamna Abiodin ya miƙa sakon ta'aziyya

A cikin saƙon ta’aziyyarsa, Gwamna Abiodun ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin mazan jiya, gogaggen ɗan siyasa, kuma jagora mai kishin al’umma.

Ya ce gudummawar da Sanata Otegbola ya bayar wajen ci gaban jihar Ogun da Najeriya baki ɗaya ba za a taɓa mantawa da ita ba.

Gwamnan ya jaddada cewa marigayi Otegbola ya taka rawar gani a lokacin da yake matsayin shugaban Hukumar Gidaje ta Tarayya (FHA) daga 2002 zuwa 2004.

Sanata Otegbola ya ba da gudummuwa

A cewar Abiodun, tsohon sanatan ya jagoranci hukumar FHA wajen gina gidaje masu ɗumbin yawa a faɗin Najeriya musamman a babban birnin tarayya Abuja.

Gwamnan ya ce marigayin ya yi abin a zo a ganina lokacin da yake aiki a hukumar FHA saboda kwarewar da yake da ita da kuma kishinsa na kawo ci gaba.

Kara karanta wannan

"Tinubu mutumin kirki ne, yana da niyya mai kyau," Babban malami ya yi wa mutane Nasiha

"A matsayinsa na ƙwararren mai duba fili da ƙididdigar gidaje, ya taka rawar gani wajen ayyukan gina gidaje, musamman a shirin gidaje na Gwarinpa da sauran wurare a Abuja," in ji Gwamna Abiodun.
Gwamna Abiodun.
Gwamna Abiodun ya yi addu'ar Allah ya jikan tsohon sanata Hoto: Prince Dr. Dapo Abiodun
Asali: Facebook

Gwamnan Abiodun ya ƙara da cewa jihar Ogun da ma Najeriya baki ɗaya za su yi rashin wannan babban jigo a harkokin ci gaban ƙasa.

Ya roƙi Allah Ya gafarta masa, Ya sanya shi a cikin jinƙansa, tare da bai wa iyalansa haƙurin rashinsa, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Jagoran ƙungiyar PANDEF ya kwanta dama

A wani labarin, kun ji cewa jagoran kungiyar ƴan yankin Neja Delta watau PANDEF, Cif Edwin Clark ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 97 a duniya.

Iyalan mamacin sun tabbatar da mutuwarsa a wata sanarwa da suka fitar kuma tuni suka fara shirye-shirye bukukuwan jana'iza yayin da mutane suka fara miƙa sakon ta'aziyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262