Da Gaske Sarkin Musulumi Ya Sanya Kayan Bokaye? Hoto Ya Yaɗu, An Gano Gaskiya

Da Gaske Sarkin Musulumi Ya Sanya Kayan Bokaye? Hoto Ya Yaɗu, An Gano Gaskiya

  • An gudanar da bincike kan wani hoto da ya nuna mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar sanye da kayan ƴan addinin gargajiya
  • Binciken ya nuna cewa wasu bara gurbi ne suka ɗauki hoton Sultan sanye da tufafin sarakuna na Musulunci, suka canza masa zuwa kayan bokaye
  • Hoton dai an kirkire shi ne domin yaɗa karya amma sarkin Musulmi bai sanya irin waɗannan tufafi ba kwata-kwata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Mutane da dama sun fara yaɗa wani hoto a kafafen sada zumunta na zamani wanda ya nuna mai alfarma sarkin Musulmi sanye da tufafin bokaye.

Hoton wanda ke yawo a soshiyal midiya ya nuna Sultan Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na II a cikin tufafin ƴan addinin gargajiya masu ɗauke da layu da guraye.

Sarkin Musulmi
Bincike ya nuna hoton da aka ga sarkin Musulmi sanya da kayan bokaye kirkirarre ne Hoto: Comr Anar Terfa
Asali: Facebook

Hoton ya nuna sarkin musulmi ya sa baƙar riga mai ado da ja, aska, ƙasusuwa, layu da guraye, alamomin da ake dangantawa da addinin gargajiya na Afirka.

Kara karanta wannan

"Allah ne ya jaraba mu," Gwamna ya faɗawa babban malami abin da bai sani ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan hoto, wanda aka yaɗa sosai a Facebook da shafin X watau Tuwita, ya jawo ce-ce-ku-ce.

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta, kamar Ipadabo Folashade, sun yi iƙirarin cewa ya kamata Sultan ya rungumi addinin Isese, yayin da wasu suka yi shakku kan ingancin hoton.

Sultan: An gudanar da binciken gaskiya

Binciken gaskiya da jaridar Dubawa ta gudanar tare da wasu hukumomin tantance bayanai ya gano abubuwa da dama game da hoton.

Na farko an gano cewa an jirƙita hoton ta hanyar amfani da fasahar gyaran hoto ta zamani, inda aka sanyawa mai alfarka sarkin Musulmi kayan bokayen.

Amma a asalin hoton an gano cewa Sultan yana cikin tufafin gargajiyarsa na Musulunci kamar yadda aka saba ganinsa da rawani, ba kayan boka ba.

Sultan na Sokoto ba kawai basarake ba ne, shi ne shugaban mabiyan addinin Musulunci a Najeriya.

Sultan ba zai taɓa sa kayan boka ba

Kara karanta wannan

Matashi ya gayyaci abokinsa gida ya masa kisan wulakanci da adda, ya sassara shi

A matsayinsa na shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ba zai yiwu ya yi irin wannan shiga ba.

Bugu da ƙari, babu wata sahihiyar kafar yada labarai da ta ruwaito cewa sarkin musulmi ya sauya addini ko ya sanya kayan ƴan addinin gargajiya.

Haka nan masarautar mai alfarma sarkin Musulmi ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Sarkin Musulmi.
Sarkin Musulmi bai taɓa sa kayan bokaye ba Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Getty Images

Kammalawa

Hoton ake yaɗawa a kafafen sada zumunta wanda ke nuna Sultan na Sokoto yana sanye da kayan boka ba gaskiya ba ne.

An canza hoton ne ta hanyar fasahar gyaran hoto domin yada ƙarya. Ya kamata masu amfani da kafafen sada zumunta su dinga tantance ingancin labari kafin su yada shi.

Sarkin Musulmi ya jagoranci rabon Zakkah

A wani labarin, kun ji cewa sarkin Musulmi ya jagoranci zakkar miliyoyin Naora a Haɗeija da ke jihar Adamawa.

mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa’adu Abubakar III, ya yabawa gwamnan Jigawa, Umar Namadi bisa gudunmawar da ya ke bayarwa ga addinin Musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262