Bayan Ya Kirkiro Sababbin Masarautu, Gwamna Ya Tsige Wasu Sarakuna daga kan Mulki
- Gwamna Ahmadu Fintiri ya sallami dukkan hakimai da masu rike da sarauta a yankunan da ya kafa sababbin maarautu a Adamawa
- Fintiri ya bukaci su garzaya su yi mubaya'a ga sababbin sarakunan da ya naɗa, yana mai cewa matakin da ya ɗauka ya fara aiki nan take
- Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Fintiri ya kirkiro sababbin masarautu bakwai, lamarin da ake ganin ya rage ƙarfin Lamidon Adamawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Adamawa - Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya kori dukkan hakimai da masu rike da sarautun gargajiya a yankunan sababbin masarautun da ya ƙirƙiro a jihar.
Gwamna Fintiri ya sanar da hakan ne a ranar Laraba a garin Gulak, yayin da yake mika sandar mulki ga sabon sarkin Madagali, Ali Danburam.

Asali: Twitter
Gwamna ya tsige hakimai a Adamawa
Jaridar Premium Times ta tattaro cewa gwamnan ya umarci hakiman da sauran masu sarauta a sabbabbin masarautun su ajiye rawani nan take.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Dukkan hakimai da masu rike da sarautun gargajiya da aka naɗa a tsohon tsarin masarautu, su sauka daga mukamansu nan take."
"Ina kira ga hakiman da abin ya shafa da su koma sababbin masarautun da muka kawo, su yi mubaya'a ga sababbin sarakuna," in ji Gwamna Fintiri.
Sababbin masarutun da gwamna ya kirkiro
A cikin watan Disamba, Gwamna Fintiri ya kafa sababbin masarautu guda bakwai, wanda hakan ya sa jimillar masarautun gargajiya a jihar suka zama 14.
Majalisar dokokin jihar ta amince da sabuwar dokar nadawa da sauke sarakuna a ranar 10 ga Disamba, kwana daya bayan gabatar da kudirin.
Sauye-sauyen sun rage yankin ikon Lamidon Adamawa, Mustapha Barkindo, daga kananan hukumomi 8 zuwa 4 (Yola ta Kudu, Yola ta Arewa, Girei, da Hong).

Kara karanta wannan
Adamawa: 'Yan ta'adda sun kai hari babban asibiti, an yi awon gaba da bayin Allah
Hakazalika, Sarkin Mubi, Abubakar Isa-Ahmadu, yanzu yana da kananan hukumomi 2 (Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu), maimakon 5 da yake da su a baya.
Jerin sababbin masarautun Adamawa
Sababbin masarautu da mai girma gwamnan Adamawa ya kirkiro sun hada da:
1. Masarautar Huba – Hedikwata a Hong (Sarki mai daraja ta biyu).
2. Masarautar Madagali – Hedikwata a Gulak (Sarki mai daraja ta biyu).
3. Masarautar Michika – Hedikwata a Michika (Sarki mai daraja ta biyu).
4. Masarautar Fufore – Hedikwata Fufore (Sarki mai daraja ta biyu).
5. Masarautar Gombi – Hedikwata a Gombi (Sarki na aji na uku).
6. Masarautar Yungur – Hedikwata a Dumne (Sarki na aji na uku).
7. Masarautar Maiha – Hedikwata: Maiha (Sarki na aji na uku).

Asali: Twitter
Sabuwar dokar masarautu a Adamawa
Sabuwar dokar masarautun Adamawa ta bai wa gwamna damar sauke sarki idan yana fama da rashin lafiya ko ya samu naƙasa.
Sashe na 6(e) na dokar ya ce:
"Idan aka tantance sarki ya kamu da rashin lafiya mai hana shi iya tafiyar da masarautarsa, bayan binciken kwamitin likitoci na Ma'aikatar Lafiya, kuma Majalisar zartarwa ta amince, gwamna na da ikon sauke shi."
A halin yanzu Gwamna Fintiri ya tsire dukkan hakimai da masu rike da sarauta a sababbin masarautun da ya kafa, ya kuma nemi su yi mubayi'a ga sarakunan da ya naɗa.
Gwamna Fintiri ya naɗa sarkin Fufore
Kun ji cewa Gwamna Ahmadu Fintiri ya nada Alhaji Muhammadu Sani Ahmadu Ribadu, ɗan uwan Nuhu Ribaɗu a matsayin Sarkin Fufore a Adamawa.
Masarauyar Fuforr na ɗaya daga cikin sababbin masarutu bakwai da gwamnan ya ƙirkiro, waɗanda ya ce za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya.
Asali: Legit.ng