"Wa Ya Mata Cikin?": Jarumar Fim a Najeriya Ta Yi Magana Kan Zargin Sanata Ya Mata Ciki

"Wa Ya Mata Cikin?": Jarumar Fim a Najeriya Ta Yi Magana Kan Zargin Sanata Ya Mata Ciki

  • Jarumar masana'antar fim watau Nollywood, Chika Ike ta musanta raɗe-raɗin cewa cikin da take ɗauke da shi na Sanata Ned Nwoko ne
  • Fitacciyar jarumar ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa da attajirin kuma ɗan siyasa, sannan ba ta da shirin auren mutum mai mata
  • Wannan dai na zuwa ne bayan Sanata Nwoko, wanda bai jima da komawa APC ba, ya musanta zargin yana shirin auren jarumar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta - Fitacciyar jarumar Nollywood, Chika Ike, ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa sanata kuma attajiri, Ned Nwoko, ne uban ɗan cikin da take dauke da shi.

Sanata Ned Nwoko, wanda yake auren jaruma Regina Daniels, ya karyata wannan ikirari a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na sada zumunta a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Sanata ta riiga mu gidan gaskiya bayan an mata tiyata a ƙasar Amurka

Jaruma Chika Ike.
Jarumar Chida Ike ta musanta rade-radin cewa Sanata Nwoko ne ya mata ciki Hoto: Chika Ike
Asali: Facebook

A ranar Talata, Chika Ike ta wallafa a shafin ta na Facebook cewa cikin da take ɗauke da shi ba na Sanata Nwoko ba ne kamar yadda ake ta yaɗa jita-jita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jarumar ta kuma bayyana cewa ba ta niyyar zama matar sanatan ta bakwai domin ba ta sha'awar zaman kishiyoyi da wasu matan.

Jarumar fim ta yi bayani kan jita-jitar

Chika Ike ta ce shekaru da dama mutane suna yayata jita-jita marasa tushe game da rayuwarta, amma wannan batun ya shafi yaronta ne, don haka dole ne ta yi martani.

"A tsawon shekaru, mutane suna yada karya a kaina a kafafen sada zumunta, amma ba na daukarsu da muhimmanci. Amma wannan lamari ya bambanta, saboda ya shafi yarona.
"Babu wanda ya san komai a kaina, kuma ba wanda zai sani sai idan na yanke shawarar bayyana hakan. Eh, ina da sirri sosai!"
"Ned ba shi ne uban ɗan da ke cikina ba kuma duk abin da za ku faɗa na hasashe, ina tabbatar maku da cewa ni ba zan taba zama matarsa ta bakwai ba, babu ruwana da auren mai mata da yawa."

Kara karanta wannan

"Ba sabani aka ba," Naburaska ya fadi dalilin watsi da Kwankwasiyya

Wa ya yi wa jarumar ciki?

Jarumar ta bayyana cewa mutane ba su san komai game da ita ba, domin ta boye ciki na tsawon watanni ba tare da wani ya sani ba, har sai da ta bayyana hakan da kanta.

"Na dauki ciki tsawon watanni ba tare da kowa ya sani ba, sai da na sanar da kaina. Yanzu kuma kuna tunanin za ku san uban cikin ko wani abu game da rayuwata? Wannan abin dariya ne kuma mara tushe," in ji ta.

Jaruma Chika Ike ta yi watsi da masu yada wannan jita-jita, tana mai cewa tana jin dadin cikinta kuma hakan ne kadai ke da muhimmanci a gare ta.

Ta bukaci masu yada wannan labari su ci gaba da bincike, domin kuwa ba za su taba samun wata gamsasshiyar amsa daga gare ta kan uban ɗanta ba.

Gwamna Diri ya musanta alaƙa da Nengi

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Bayelsa, Douye Diri ya karyata jita-jutar da ake yaɗawa cewa cikin da jarumar BBN, Nengi Hampson ke ɗauke da shi nasa ne.

Gwamnan ya bayyana cewa ba shi da waya alaƙa ta musamman da jarumar, inda ya bayyaɓa rahoton da ake yaɗawa a matsayin kagaggen labari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262