Rumbun Sauki: Gwamna Ya Bude Wuraren Sayar da Abinci da Araha ga Talakawa

Rumbun Sauki: Gwamna Ya Bude Wuraren Sayar da Abinci da Araha ga Talakawa

  • Gwamna Dikko Radda ya kaddamar da shirin ‘Rumbun Sauki’ domin rage wahalar abinci da inganta tattalin arziki
  • Gwamnatin jihar ta ware sama da N4bn don sayen kayan masarufi da za a sayar wa ma’aikata da al'umma da rangwame
  • Ana sa ran shirin zai bunkasa tattalin arziki inda masu sayar da kaya za su samu ciniki da zai kai fiye da N50bn a kowace shekara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta dauki matakin dakile matsalar karancin abinci ta hanyar kaddamar da shirin sayar da kayan masarufi da rangwame na ‘Rumbun Sauki’.

Shirin, wanda Gwamna Dikko Radda ya kaddamar, yana da nufin taimakawa ma’aikata, tsofaffin ‘yan fansho da mazauna jihar wajen samun abinci a farashi mai rahusa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun farmaki maboyar wani babban dan bindiga, an kashe 'yan ta'adda 53

Radda
Gwamnatin Katsina za ta fara sayar da abinci da araha. Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed ya wallafa a Facebook cewa Dikko Radda ya ware N4bn don aiwatar da shirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika Ibrahim Kaula Mohammed ya ce shirin zai fara aiki a manyan garuruwan Katsina, Daura da Funtua.

An kafa cibiyoyin sayar da kayan abinci

Gwamna Radda ya bayyana cewa shirin zai fara ne da cibiyoyi bakwai, inda uku za su kasance a garin Katsina, biyu a yankin Daura, sannan biyu a yankin Funtua.

Haka zalika gwamnan ya ce an dauki tsauraran matakai don tabbatar da gaskiya da adalci a gudanar da shirin.

Gwamnan ya gargadi masu gudanar da shirin cewa duk wanda aka samu da aikata ba daidai ba, zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Na'ukan abinci da za a sayar a Katsina

Mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal Jobe, ya jaddada cewa shirin zai kara habaka tattalin arzikin jihar inda 'yan kasuwa za su samu riba sosai.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kwaikwayi Abba Kabir na Kano, ya rabawa mata awaki 40,000

Kwararre a fannin bunkasa tattalin arzikin karkara, Yakubu Nuhu Danja, ya ce kayayyakin abinci da za a sayar a karkashin shirin sun hada da shinkafa, alkama, masara da taliya

Masana na ganin shirin zai kawo saukin ga al'umma musamman a yanzu da ake kokarin fara azumin watan Ramadan na shekarar 2025.

Yadda mutum zai saye abinci a rumbun sauki

Dr Shuaibu Mohammed na kamfanin wanda shi ne mai kula da shirin, ya bayyana cewa an samar da tsarin rajista na zamani domin ba al'umma damar sayen abinci.

A cewarsa, duk wanda yake son cin gajiyar shirin zai yi rajista ta intanet sannan ya biya kudin kayayyaki ta hanyar ATM, monie point ko wasu hanyoyin sadarwa na zamani.

A cikin watan Oktoba 2024, Gwamna Radda ya bayyana kudirinsa na yin koyi da shirin tallafin abinci da aka aiwatar a jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Ramadan cikin sauki: Za a rabawa talakawa tirelolin abinci 500 kyauta a Neja

Martanin shugabannin 'yan kwadago

An ruwaito cewa shirin ‘Rumbun Sauki’ ya samu amincewa daga shugabannin ma’aikata da kungiyoyin kwadago.

Shugaban kungiyar NLC reshen Katsina, Husaini Hamisu Yanduna, da shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Falalu Bawale, sun yaba da shirin.

Sun ce wannan mataki zai rage radadin halin matsin tattalin arziki da ma’aikata da ‘yan fansho ke fuskanta.

Gwamnatin Katsina ta yabi sojoji

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta yabawa dakarun sojin Najeriya bisa ragargazar 'yan bindiga.

Sojojin sun kai farmaki kan 'yan bindiga ne yayin da suke kokarin kulla makirci, kuma sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda 53.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng