Al'umma Sun Taso Sarki da Ya Yi Batan Dabo a Gaba Yayin da Matarsa Ke Sarauta
- Rashin sanin halin da Basarake Oba Joseph Olugbenga Oloyede a jihar Osun ya tayar da hankulan al'umma
- Rahotanni sun tun Maris din 2024 babu duriyarsa inda al'ummar Ipetumodu ke neman bayanin inda yake
- Wasu na zaton yana jinya a Amurka, amma wasu na kyautata zaton yana fuskantar shari'ar zamba kan kudin tallafin COVID-19
- An bayyana cewa ya samu $4.2bn ta hanyar bogin kamfanoni, tare da wani mai suna Edward Oluwasanmi, wanda ake tuhuma a Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Osogbo, Osun - An shafe watanni babu labarin Oba Joseph Olugbenga Oloyede, Apetu na Ipetumodu a jihar Osun.
Mazauna yankin sun roki Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, da ya binciki lamarin.

Asali: Original
Al'umma sun bukaci bayani kan sarkinsu
Punch ta ce Oba Oloyede na zaune a Amurka, an nada shi sabon Apetu a watan Yulin 2019 bayan rasuwar Oba James Adegoke a 2017.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun bayan nadinsa, ya kan rika tafiye-tafiye tsakanin Najeriya da Amurka, amma tun daga Maris 2024 da ya tafi bai dawo ba.
Wasu daga cikin mazauna garin sun ce suna jin yana jinya a Amurka, amma wasu na zaton yana fuskantar shari'ar damfara kan kudaden COVID-19.
Wani babban mutum a Ipetumodu ya bayyana cewa tun kusan shekara daya ba a ga Sarki a garin ba, kuma yana rasa tarukan al'umma.
A lokacin addu'ar Kiristocin Ipetumodu, an ga wanda aka ce shi ne Oba Oloyede a hoton bidiyo, amma fuskarsa ba ta bayyana sosai ba.
Oba Oloyede ya yi alkawarin dawowa kafin ƙarshen watan Janairun 2025 amma yanzu Fabrairu ta zo ba a gan shi ba.
Ana zargin ya rusa tsohon fadar sarauta kuma ya yi alkawarin gina sabuwa, amma har yanzu ba a ga sabon ginin ba.
Zargin da ake yi wa basaraken a Amurka
Rahotanni sun nuna cewa bai halarci bukukuwan gargajiya guda uku na garin ba, wanda hakan ya jawo rudani a tsakanin jama'a.
Wata majiya ta ce matar Sarki ce ke gudanar da harkokin mulki a madadinsa, lamarin da ke sa jama'a tambayar inda yake.
Rahotanni daga Amurka sun nuna cewa ana tuhumarsa da damfara kan kudaden tallafin COVID-19 na dala miliyan 4.2 tare da wani mai suna Oluwasanmi.
A wata hirar bidiyo, Oba Oloyede ya karyata jita-jitan cewa yana fuskantar shari'a, yana mai cewa maganganun makiya ne kawai.
Bayan nada sabon Sarki, rigima ta balle
Kun ji cewa sabuwar rigima ta barke a garin Esa-Oke da ke Osun bayan nadin Yarima Timileyin Oluyemi Ajayi a matsayin Olojudo na Ido Ayegunle.
Wasu da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki cikin garin, suka bude wuta kan jama’a, lamarin da ya jawo asarar rayuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng