Mutuwar Mutane a Hadarin Kano Ya Girgiza Jama'a, Sanata Barau Ya yi Ta'aziyya

Mutuwar Mutane a Hadarin Kano Ya Girgiza Jama'a, Sanata Barau Ya yi Ta'aziyya

  • Hukumar kiyaye hadurra ta kasa ta tabbatar da cewa mutane 23 sun rasa rayukansu a wani hadarin mota da ya afku a karkashin gada a Kano
  • Rahotanni sun tabbatar wa Legit cewa mummunan hadarin ya faru ne yayin da motar ta nufi titin Kano-Maiduguri a unguwar Hotoro
  • Sanata Barau Jibrin ya bayyana alhinin sa kan lamarin tare da mika ta'aziyya ga iyalan mamatan, yana rokon Allah ya jikansu da rahama
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya kuma bukaci direbobi su kasance masu bin dokokin hanya domin gujewa irin wannan hadari a gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Wani mummunan hadari ya afku a titin Kano-Maiduguri yayin da birkin tirela ya tsinke, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 23 tare da jikkata wasu da dama.

Kara karanta wannan

Canada ya yi martani kan rahoton hana hafsan tsaron Najeriya shiga kasarta

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa hadarin ya jawo babban rashi ne ga iyalan wadanda suka rasu da al'umma gaba daya.

Barau
Sanata Barau ya yi ta'aziyyar mutane da suka rasu a hadarin Kano. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Twitter

Legit ta gano cewa Sanata Barau Jibrin ya wallafa sakon ta'aziyya kan rashin da ya girgiza mutane a Kano da Najeriya ne a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ce ta sanar da yawan mutanen da suka rasa rayukansu, inda ta bukaci direbobi da fasinjoji su rika kiyaye dokokin hanya.

Ta'aziyyar Sanata Barau ga mutanen Kano

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya nuna alhinin sa bisa babban rashin da ya rutsa da mutane 23 a jihar Kano.

Sanata Barau ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu tare da addu'ar Allah ya jikansu da rahama.

Sakon da Sanatan ya wallafa ya kunshi cewa:

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Na yi juyayin wannan hadari da ya auku a karkashin gadar Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Birkin tirela ya tsinke a Kano, ta murkushe mutane da dama

"Allah ya jikansu da rahama, ya ba iyalansu hakuri da juriya."

Barau Jibrin ya kara da cewa yana rokon Allah (SWT) ya bai wa wadanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa.

Barau ya ce bukatar bin dokokin hanya

Sanata Barau Jibrin ya bukaci direbobi su kasance masu kula da dokokin hanya domin gujewa irin wannan hadari a nan gaba.

A cewarsa:

"Wannan lamari yana tunatar da mu bukatar yin taka-tsantsan a hanya da bin dokokin tuki."

Ya ja hankalin masu abubuwan hawa da su rika kiyaye ka'idojin tuki, kamar rage gudu da kaucewa tukin ganganci domin kare rayukan jama'a.

Addu'o'in jama'a ga mamatan

Bayan faruwar wannan mummunan hadari, mutane da dama sun nuna alhinin su tare da yin addu’o’i ga mamatan da iyalansu.

Baya ga haka, jama'a sun bukaci gwamnati ta kara daukar matakan kare lafiyar direbobi da fasinjoji a tituna.

Haka zalika, an yi kira ga hukumomi su tabbatar da ganin an kara wayar da kai kan bin dokokin hanya domin rage yawan hadurra a kasar nan.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

Barau Jibrin zai raba tallafin noma

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Barau Jibrin zai raba tallafin noma ga matasan yankin Arewa maso Yamma.

A karkashin shirin, Sanata Barau zai raba tallafin Naira biliyan 2.79 ga matasan domin farfado da noma da yaki da yunwa a yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng