Mutuwa Ta Ƙara Girgiza Najeriya, Jagoran Afenifere Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Jagoran ƙungiyar Afenifere mai kare al'adun yarbawa a Najeriya, Pa Ayodele Adebanjo ya mutu yana da shekaru 96 a duniya
- A wata sanarwa da iyalansa suka rattaɓawa hannu, marigayin ya mutu ne a safiyar yau Juma'a, 14 ga watan Fabrairu, 2025
- Iyalan sun bayyana cewa za su sanar da tsare-tsaren yadda za a masa jana'iza bayan sun gama tuntuɓar ƴan uwa da abokan arziki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Tsohon babban jigon siyasa kuma shugaban kungiyar yarbawa watau Afenifere, Pa Ayodele Adebanjo, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 96.
A cewar iyalansa, Pa Adebanjo ya rasu da safiyar ranar Juma’a, 14 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke Lekki a jihar Lagos.

Asali: Facebook
Iyalan sun sanar da rasuwar jagoran Afenifere ne a wata sanarwa da suka fitar yau Juma'a, 14 ga watan Fabrairu, 2025, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Iyalan Adebanjo sun sanar da rasuwarsa
A cikin sanarwar, iyalan sun bayyana cewa:
“Ya rasu cikin lumana da safiyar yau, Juma’a, 14 ga watan Fabrairu, 2025, a gidansa da ke Lekki, Lagos. Za mu ci gaba da tunawa da kishinsa a kan gaskiya, adalci da daidaito.
“Ya sadaukar da rayuwarsa wajen fafutukar ganin Najeriya ta zama ƙasa mai ‘yanci da ci gaba. Ya ci gaba da wannan gwagwarmaya har zuwa karshen rayuwarsa.”
Sanarwar na ɗauke da sa hannu a madadin Mrs. Ayotunde Atteh (nee Ayo-Adebanjo), Mrs. Adeola Azeez (nee Ayo-Adebanjo) da kuma Mr. Obafemi Ayo-Adebanjo.
Iyalan sun ce suna shirin sanar da cikakken jadawalin jana’iza bayan sun tattauna da abokai da makusantan mamacin.
Za a bude rajistar ta’aziyya a gidansa da ke Lekki, Lagos da kuma Isanya Ogbo, kusa da Ijebu Ode a jihar Ogun.
Takaitaccen tarihin marigayi Ayo Adebanjo
Pa Ayodele Adebanjo shahararren lauya ne kuma tsohon sakataren shirye-shirye na jam’iyyar Action Group.
Ya kasance jigo a tafiyar siyasar Yarbawa kuma babban jagoran kungiyar Afenifere, in ji rahoton The Nation.
Ya bar duniya yana da mata ɗaya, Chief Christy Ayo-Adebanjo, da yara, jikoki, da tattaba-kunne.
Tuni dai manyan mutane da ƴan uwa da abokan arziki suka fara tura saƙon ta'aziyya tare da addu'ar samun salama.
Tsohon dogarin Obasanjo ya kwanta dama
A wani rahoton, kun ji cewa Allah ya yi wa Manjo Janar Chris Jemitola (mai ritaya), tsohon dogari ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, rasuwa.
Rahoto ya nuna cewa Jemitola ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya fadi a babban filin wasan golf na Ibrahim Badamasi Babangida da ke Abuja a safiyar Alhamis.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng