An Shiga Fargaba da Aka Kama Tulin Makamai Ana Yunƙurin Shigo da Su Najeriya

An Shiga Fargaba da Aka Kama Tulin Makamai Ana Yunƙurin Shigo da Su Najeriya

  • Jami'an hukumar kwastam sun yi nasarar cafke wasu manyan makamai da aka shigo da su cikin ƙasar nan ta jihar Legas
  • Rahotanni sun nuna shugaban hukumar kwastam ta Najeriya (NCS), Adewale Adeniyi ya isa Legas domin zantawa da manema labarai
  • Wannan ba shi ne karo na farko da kwastam ke kama makamai ba a daidai lokacin da ake fama da matsalolin tsaro a sassa daban-daban

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Lagos - Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta kama adadi mai yawa na bindigogi da alburusai da aka shigo da su ƙasar nan ba bisa ƙa'ida ba a jihar Legas.

Ko da yake ba a bayyana ƙimar waɗannan makamai ba tukuna, an tabbatar da cewa adadin su yana da yawan gaske.

Shugaban kwastam.
Jami'an kwastam sun kama makamai ana shirin shigo da su cikin ƙasa a Legas Hoto: NCS
Source: Facebook

Kwanturola Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya isa Legas domin yi wa manema labarai bayani a Ofishin ayyuka na ƙasa (FOU) da ke Ikeja, in ji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

Kwastam suna yawan kama makamai

Wannan nasara na zuwa ne a daidai ne lokacin da ake fama da matsalar tsato kama daga ƴan bindiga, ƴan fashin daji, da sauransu a sassan ƙasar nan.

Ba wannan ne karon farko da dakarun hukumar kwastam ke kama makamantan irin waɗannan makaman da ake shirin shigo da su Najeriya ba.

A cikin watan Yulin 2024, jami'an kwastam sun kama fiye da bindigogi 800 da alburusai 100,000 da aka ɓoye a cikin kwantena a tashar jiragen ruwa.

A shekaru da da dama da suka gabata, Hukumar Kwastam ta yi nasarar kama makamai da alburusai masu ɗumbin yawa daga hannun masu fasa kwaurinsu.

Yadda kwastam ke ba da gudummuwa

A cewar rahoton da aka fitar a watan Oktoba 2024, hukumar ta kama makamai 10,498 da alburusai 114,929 tun daga shekarar 2018, wanda darajar su ta kai Naira biliyan 9.58.

Kara karanta wannan

Katsina: Likitan da ke kula da lafiyar 'yan ta'adda ya shiga hannun jami'an tsaro

Bayanai sun nuna cewa kashi 60% na makaman da kwastam suka cafke ana shirin shigo da su Najeriya, an kama su ne a bara.

Waɗannan nasarori suna nuna ƙoƙarin da Hukumar Kwastam ke yi wajen hana shigo da makamai ba bisa ƙa'ida ba, wanda hakan na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro a ƙasar nan.

Nasarorin jami'an kwastam a shekarar 2024

A wani labarin, kun ji cewa hukumar kwastan ta Najeriya (NCS), ta bayyana cewa jami'anta sun kama motoci 397 da darajarsu ta kai Naira biliyan 5.64 a 2024.

Hukumar ta ƙara da cewa bayan wannan, ta kuma kama magunguna 175,676 da kwantena 6,271 na jabun magunguna da darajarsu ta kai Naira biliyan 3.04.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262