Ajali Ya Yi: Gwamna Ya Kaɗu da Mai Martaba Sarki Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Ajali Ya Yi: Gwamna Ya Kaɗu da Mai Martaba Sarki Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun ya bayyana kaduwarsa da rasuwar sarkin Iperu-Remo, Oba Adeleke Adelekan Idowu-Basibo
  • Abiodun, wanda ke da sarauta a masarautar marigayin, ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin rashi da zai wuya a maye gurbinsa
  • Al'ummar yankin masarautar Iperu-Remo sun fara jimamin wannan rashi na uba da suka yi a jihar Ogun

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Gwamnan Ogun, Prince Dapo Abiodun, ya yi alhinin mutuwar Sarkin Iperu-Remo, Oba Adeleke Adelekan Idowu-Basibo.

Gwamna Abiodun ya bayyana mutuwar basaraken a matsayin babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba.

Gwamna Dapo Abiodun.
Gwamnan Ogun ya yi ta'aziyyar rasuwar sarkin Iperu-Remo, Oba Adeleke Adelekan Idowu-Basibo Hoto: Prince Dapo Abiodun
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Gwamna Abiodun ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, 2025.

Gwamna Abodun ya kaɗu da rashin sarkin Iperu-Remo

Abiodun ya ce mutuwar basaraken ta girgiza shi matuka saboda yadda yake da kusanci da shi da kuma kyawawan halayensa.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: An taso Tinubu a gaba, malami ya buƙace shi don Allah ya yi murabus

Gwamna Abiodun ya ce ya amince da ikon Allah, wanda ba mai iya jayayya da hukuncinsa kan rayuwar kowane dan Adam.

Gwamnan, wanda ke da sarauta ne a masarautar Iperu-Remo, ya bayyana marigayin a matsayin shugaba nagari da ya kawo zaman lafiya da ci gaban yankin.

Dapo Abiodun ya ce:

"Oba Adeleke Adelekan Idowu-Basibo mutum ne mai cikakken kamala. Ya yi karatun firamare a makarantar St. James, daga nan ya wuce kwalejin fasaha ta Ibadan. Ya karanci fannin Marine Economics a jami'ar London."

Sarkin ya ba da gudummuwa a rayuwarsa

Gwamnan ya jaddada cewa mulkin basaraken ya kawo ci gaba mai yawa a Iperu-Remo, musamman a bangaren gina ababen more rayuwa, bunkasar tattalin arziki da wanzar da zaman lafiya.

Ya kara da cewa:

"Oba Idowu-Basibo mutum ne mai ladabi da mutunci, wanda ya kula da jin dadin jama’arsa ba tare da la’akari da bambancin addini ko siyasa ba. Za a yi matukar kewarsa."

An bayyana Oba Adeleke Adelekan Idowu-Basibo a matsayin mutum mai ilimi da gogewa, wanda ya yi aiki a Hukumar Kwastam ta Turai na tsawon shekaru 20 kafin ya zama Sarki.

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa 6 da suka fi ƙoƙari wajen samar da matakan tsaro na kansu

Al'ummar Iperu-Remo da daukacin jihar Ogun suna ci gaba da jimamin wannan babban rashi.

Gwamnan Ogun ya dakatar da basarake

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Dapo Abiodun ya dakatar da sarkin Orifo Ifo, Oba Abdulsemiu Ogunjobi daga sarauta saboda cin mutuncin dattijo.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Hon Ganiyu Hamzat, ya sanya wa hannu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262