Mummunar Gobara Ta Tashi a Kano, Ta Jawo Gagarumar Asara

Mummunar Gobara Ta Tashi a Kano, Ta Jawo Gagarumar Asara

  • Wata mummunar gobara da ta tashi a jihar Kano a ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairun 2025 ta jawo asarar dukiya mai tarin yawa
  • Gobarar ta laƙume manyan gidaje guda biyu yayin da ta ƙona dabbobi masu yawa da suka haɗa da shanu da awaki
  • Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce jami'anta sun yi ƙoƙarin hana wutan yaɗuwa zuwa sauran gidaje

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - An samu tashin wata mummunar gobara a ƙauyen Danzago da ke ƙaramar hukumar Danbatta a jihar Kano.

Mummunar gobarar ta laƙume gidaje biyu, tare da ƙona dabbobi bayan ta tashi a ranar Larabar nan da ta gabata.

Gobara ta yi barna a Kano
Mummunar gobara ta yi barna a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da aukuwar lamarin, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gobara ta tashi a kauyen Kano

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga sama da 100 suka taru wajen sace Janar Tsiga a Katsina

Hukumar ta bayyana cewa ta samu rahoton tashin gobarar ne ta hannun wani mai suna Abdurashid Sha’aibu da misalin ƙarfe 10:48 na safe.

Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce jami’an kashe gobara daga sashen Danbatta sun isa wurin da gobarar ta tashi da misalin ƙarfe 11:22 na safe.

A cewar Saminu Abdullahi, gobarar ta fara ne a wani babban gida da ake kira da Gidan Ado Yubai, wanda ke ɗauke da dakuna 17, ɓangarori tara da rumbuna.

A sanadiyyar tashin gobarar, shanu biyu, tumaki 36, awaki 17, kaji 10 da kuma rumbuna 19 na ajiyar kayan abinci sun ƙone ƙurmus.

Jami'ai sun ceto wasu kayayyaki

Sai dai jami’an kashe gobara sun samu nasarar ceto tumaki biyu, shanu huɗu, rumbuna biyu na ajiyar abinci da wasu kayayyaki.

Saminu Abdullahi ya ƙara da cewa wutar ta ci gaba da yaɗuwa zuwa wani babban gida da ake kira Gidan Ibrahim Mai Gariyo, inda ta lalata ɗakuna, ta ƙona rumɓu ɗaya, sannan ta kashe tumaki takwas da awaki uku.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya yi alhinin rasuwar Almajirai a gobara, ya fadi matakin ɗauka

Kakakin hukumar ya ce jami’an kashe gobara sun samu nasarar ceto rumbu ɗaya da wasu kayayyaki, lamarin da ya hana gobarar bazuwa zuwa gidajen makwabta.

Ba a samu asarar rayuka a gobarar ba?

Ya ƙara da cewa wani jami’in hukumar ya ƙone a ƙafarsa yayin da yake ƙoƙarin shawo kan gobarar, amma ba a sanu asarar rai ba.

Ya kuma bayyana cewa saboda girman gobarar, sai da aka tura jami'ai daga Danbatta da Dawanau domin shawo kanta.

Saminu Abdullahi ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.

Gobara ta ƙona Almajirai cikin dare

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin wata mummunar gobara a wata makarantar allo da ke jihar Zamfara, har shugaban kasa ya yi magana.

Gobarar wacce ta tashi da tsakar dare a makarantar allon da ke ƙaramar hukumar Kauran Namoda, ta jawo asarar rayukan Almajirai fiye da guda 10.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta tashi a makarantar allo, an samu asarar rayukan dalibai

Wasu daga cikin ɗaliban da lamarin ya ritsa da su an yi gaggawar kai sun asibiti sakamakon raunukan da suka samu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel