Gwamnan Zamfara Ya Yi Alhinin Rasuwar Almajirai a Gobara, Ya Fadi Matakin Dauka
- Ana ci gaba da jimami tare da alhinin rasuwar wasu Almajirai a wata makarantar allo da ke ƙaramar hukumar Kauran-Namoda ta jihar Zamfara
- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa.ga iyalan waɗanda suka rasu sakamakon gobarar da ta tashi a makarantar
- Ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta yi bincike domin gano dalilin tashin gobarar domin ɗaukar matakan hana aukuwar hakan a nan gaba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan Almajiran da suka rasu sakamakon gobara a jihar.
Gwamna Dauda Lawal ya nuna alhininsa kan rasuwar ɗaliban sakamakon gobarar da ta tashi a wata makarantar allo a jihar.

Source: Twitter
Gwamnan jihar Zamfara ya yi ta'aziyya
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

Kara karanta wannan
Gwamna ya gano badaƙalar kudi, ya dakatar da kwamishina da shugaban hukuma nan take
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ƙalla Almajirai 17 ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar gobarar da ta tashi a wata makarantar allo da ke ƙaramar hukumar Kaura-Namoda a jihar.
Dauda Lawal ya bayyana mummunan lamarin tashin gobarar a matsayin abin takaici matuƙa.
Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don tallafawa waɗanda suka rasa ƴan uwansu da kuma mutanen da gobarar ta shafa.
Gwamna Dauda ya umarci a yi bincike
Ya kuma buƙaci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike mai zurfi don gano haƙiƙanin dalilin tashin gobarar da kuma hanyoyin da za a bi domin hana sake faruwarta a nan gaba.
“Ina cikin juyayi da damuwa sakamakon gobarar da ta tashi a ranar Talata a makarantar Malam Ghali, wata makarantar Almajirai da ke ƙaramar hukumar Kaura-Namoda."
“A madadin gwamnatin jihar Zamfara, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalan mamatan, makarantar da kuma ɗaukacin al’ummar ƙasar nan yayin da muke alhinin rasa rayukan waɗannan matasan."
“A cikin wannan lokaci na baƙin ciki, muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya ba iyalan da suka yi rashi ƙarfin hali da hakurin jure wannan babban rashin. Haka nan, muna addu’ar samun sauƙi cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata."
“A matsayinmu na gwamnati mai kishin al’umma, za mu binciki musabbabin tashin wannan gobara domin gano matakan da za a ɗauka don hana faruwar irin wannan musiba a nan gaba."
“Za mu samar da dukkanin tallafi da taimakon da ya dace ga iyalan waɗanda abin ya shafa."
- Gwamna Dauda Lawal
Gwamnan Zamfara ya ɗauki matasa aiki
A wani labarin kuma kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ɗauki ɗaliban da suka kammala karatu a fannin jinya a daga ƙasar Sudan aiki.
Gwamna Dauda ya ɗauki ɗaliban su 16 waɗanda suka kammala karatu a jami'ar ƙasa da ƙasa da ke ƙasar Sudan.
Ɗaliban dai sun kasance daga cikin waɗanda aka ceto daga ƙasar Sudan biyo bayan yaƙin da ya ɓarke.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
