Dan Bello Ya Magance Matsalar Ruwa a Kauyukan Katsina, Ya Jefa Kalubale ga Buhari

Dan Bello Ya Magance Matsalar Ruwa a Kauyukan Katsina, Ya Jefa Kalubale ga Buhari

  • Shahararren mai yin barkwanci a kafafen sada zumunta, Dan Bello, ya gina rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana a ƙauyuka biyu na Katsina
  • Rijiyar ta ci kuɗi N4.3m kuma ta taimaka wajen kawar da matsalar rashin tsaftataccen ruwan sha da al’ummar jihar suka dade suna fama da ita
  • Dan Bello ya bayyana cewa kuɗin aikin ya fito ne daga ribar da yake samu daga tallace-tallacen bidiyonsa a kafafen sada zumunta na zamani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina – Fitaccen mai yin barkwanci a kafafen sada zumunta, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Dan Bello, ya yi abin a yaba bayan ya kammala aikin rijiyar burtsatse.

Rahotanni sun nuna cewa Dan Bello ya gina rijiyar burtsaye mai amfani da hasken rana a ƙauyuka biyu na jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Rusau: Majalisar dokokin jihar Kano ta dauki zafi bayan kisan mutum 4

Dan Bello
Dan Bello ya samar da rijiyoyin ruwa a kusa da Daura. Hoto: Bashir Ahmad|Dan Bello
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka tona rijiyar ne a cikin wani bidiyo da Dan Bello ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan Bello ya kalubalanci Buhari da Sirika

Ƙauyukan da aka gina rijiyar sun haɗa da Yar Lami Santar Riga da Yar Lami Santar Lema, waɗanda ke kusa da mahaifar shugaba Muhammadu Buhari.

Haka zalika kauyukan suna kusa da mahaifar tsohon ministan harkokin sufurin jiragen saman Najeriya, Sanata Hadi Sirika.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa aikin ya taimaka wajen rage wa al’ummar da suka daɗe suna fama da matsalar rashin tsaftataccen ruwan sha wahala.

Hakan ya sanya ake ganin aikin kalubale ne ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Hadi Sirika.

Rashin ruwan sha a kauyukan jihar Katsina

Kafin gagarumin aikin da Dan Bello ya aiwatar, mazauna waɗannan ƙauyuka sun kasance suna tafiya sama da awa ɗaya domin samo ruwan sha daga wani tafki mai datti.

Kara karanta wannan

Sarki ya jefa kansa a matsala, Gwamna ya dakatar da basarake kan cin zarafin dattijo

Matsalar ta shafi rayuwar yara da manya, inda yara ke kasa zuwa makaranta saboda wahalar da ake sha wajen samun ruwa.

Fadi tashi wajen tona rijiyar burtsatse

A yayin da Dan Bello ya fara aikin rijiyar, ya fuskanci kalubale bayan na’urar tono rijiyar ta kasa cimma ruwa duk da an toni kasa har mita 65.

Matsala ta sa jama’ar ƙauyukan suka soma jin shakku, ganin yadda shugabannin siyasa da dama suka musu alkawuran da ba su cika ba a baya.

Duk da haka, Dan Bello bai karaya ba, ya ci gaba da kokari har ya kammala aikin.

A ranar 1 ga watan Fabrairu, an kaddamar da rijiyar wacce ke samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar da ke wadannan wurare.

A ina Dan Bello ya samo kudin aikin?

Dan Bello ya bayyana cewa kuɗin aikin rijiyar ya fito ne daga ribar da yake samu ta hanyar tallace-tallacen bidiyonsa a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da sarki da wasu mutane 5, sun kashe mutum 1 daga ciki

"Wannan aiki ba zai yiwu ba da ba tare da goyon bayan masoyana a kafafen sada zumunta ba.

- Dan Bello

Ya ƙara da cewa ya dauki wannan aiki a matsayin wani alhakin jagoranci na gaskiya da ya kamata duk wani ɗan Najeriya ya nuna, musamman shugabanni.

Dattawan Katsina sun yi kira ga Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa dattawan jihar Katsina sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya saki tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf.

A makon da ya wuce ne hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama Farfesa Yusuf bisa zargin rashawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel