'Yan Kasuwa Sun Sauke Farashin Fetur bayan Ragin da Dangote Ya Yi
- Farashin man fetur a wuraren manyan diloli masu zaman kansu ya sauka zuwa N925 kan kowace lita a ranar Litinin
- Rage farashin ya biyo bayan matakin matatar man Dangote da ta rage farashinta daga N950 zuwa N890 kan kowace lita
- Biyo bayan sauke farashin, ana hasashen masu gidajen mai za su rage kudin man fetur domin 'yan Najeriya sun gani a kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Abuja - Farashin man fetur a wajen manyan diloli masu zaman kansu ya ragu zuwa N925 kan kowace lita a ranar Litinin, 5 ga Fabrairun 2025.
Lamarin ya jawo ragin N27 daga farashin da aka sayar da man fetur a ranar Juma'ar da ta gabata, wanda ya kai N952 kan kowace lita.

Asali: Getty Images
Punch ta yi wani rahoto kan yadda farashin yake a gidajen mai bayan saukin da aka fara samu daga manyan 'yan kasuwar fetur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rage farashin ya biyo bayan matakin da matatar man Dangote ta dauka na saukaka farashin litar man da take saidawa daga N950 zuwa N890.
Sauyin farashin yana da tasiri sosai ga ‘yan kasuwar mai da suka riga suka sayi man a farashi mai tsada, lamarin da zai iya jefa su cikin asara mai yawa.
Yadda farashin mai ya sauka a Najeriya
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa akwai raguwar farashi a wajen mafi yawan manyan dilolin mai masu zaman kansu a fadin kasar nan.
An ruwaito cewa Nipco ya rage farashinsa zuwa N935 daga N952 da ake sayarwa a makon da ya gabata.
Haka zalika, Chipet ya saukaka farashin zuwa N935 daga N945, yayin da Aiteo ya rage farashi zuwa N925 daga N942.
Karin wuraren da suka rage kudin man fetur
A wasu wuraren manyan diloli kamar Wosbab, an ga raguwar farashi daga N947 zuwa N930, sannan Rain Oil ya rage farashi daga N947 zuwa N935.
A yankin Warri, kamfanonin Matrix da AYM Shafa sun rage farashinsu daga N970 zuwa N960 a kan kowace lita.
Tasirin rage farashin mai a Najeriya
Rahotanni sun nuna cewa wannan sauyin farashi yana da tasiri mai girma ga masu kasuwancin man fetur, musamman wadanda suka riga sun saye kaya a farashi mai tsada kafin sanarwar.
Wasu daga cikinsu za su iya sayar da man a farashin da bai kai wanda suka saya ba, lamarin da zai iya jefa su cikin asara mai yawa da ka iya kai wa miliyoyin Naira.
Gidajen mai sun sauke farashi?
Duk da wannan sauyin, har yanzu ba a ga saukin farashi a a mafi yawan wuraren saida fetur na gidajen man Najeriya ba.
Hakan na nuna cewar akwai bukatar ingantattun matakai daga hukumomin kula da harkar man fetur domin tabbatar da rage farashin.
A yanzu haka dai 'yan Najeriya za su zuba ido su ga ko gwamnati da hukumomi ko za a su dauki matakin tilasta rage kudin mai a fadin kasar nan.
Dalilin rage farashi a matatar Dangote
A wani rahoton, kun ji ce matatar Dangote da ke Legas ta yi bayani kan dalilin sauke farashin man fetur da ta yi.
Legit ta wallafa cewa matatar Dangote ta ce samun saukin farashin man fetur a Najeriya na da alaka da raguwar kudin danyen mai a kasuwar duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng