Kotu Ta ba da Sabon Umarni kan Tuhumar da EFCC Ke Yi Wa Tsohon Shugaban NHIS
- Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja ta umarci a tsare tsohon shugaban hukumar NHIS a gidan gyaran hali na Kuje
- Kotun ta ƙi amincewa da buƙatar lauyan Farfesa Usman Yusuf, ta a ci gaba da tsare shi a hannun EFCC har zuwa lokacin da za a saurari buƙatar belinsa
- Hukumar EFCC dai ta gurfanar da tsohon shugaban na hukumar NHIS a gaban kotu kan wasu tuhume-tuhume guda biyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta tura tsohon shugaban hukumar kula da inshorar lafiya ta ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, zuwa gidan gyaran hali.
Kotun yayin zamanta na ranar Litinin, ta umarci a tsare Farfesa Usman Yusuf, a gidan gyaran hali da ke Kuje.

Source: Twitter
Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu ta bayar da wannan umarni bayan an gurfanar da Usman Yusuf a gaban kotun, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
Tsohon sanata ya zubar da hawaye da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 11
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC na tuhumar tsohon shugaban NHIS
Hukumar EFCC na zargin tsohon shugaban na hukumar NHIS da saɓa ƙa'ida wajen ba kansa fifiko a tsakanin shekarun 2016 da 2017.
Haka kuma, ana tuhumarsa da bayar da kwangiloli ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba.
Hukumar EFCC ce dai ta gurfanar da Usman Yusuf kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi zargin aikata zamba da almundahana.
Sai dai, yayin da aka karanto masa tuhume-tuhumen, tsohon shugaban na hukumar NHIS ya musanta aikata dukkan zarge-zargen da ake masa.
Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar Usman Yusuf
Lauyan Farfesa Usman Yusuf, O.I. Habeeb, ya roƙi kotu da ta ba da umarni a ci gaba da tsare wanda yake karewa a hannun EFCC har zuwa lokacin da za a saurari buƙatar belinsa.
Sai dai, mai shari’a Chinyere Nwecheonwu ta ƙi amincewa da buƙatar lauyan, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.
A cewar alƙalin, da zarar an gurfanar da wanda ake tuhuma, hukumar gyaran hali ce ke da ikon ci gaba da tsare shi, ba EFCC ba.
Saboda haka, ta umarci a tura Usman Yusuf gidan gyaran hali na Kuje, inda zai ci gaba da zama har zuwa lokacin da za a saurari buƙatar belinsa.
Daga nan sai ta ɗage ƙarar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu, 2025, domin sauraron buƙatar belinsa.
Dattawan Arewa sun caccaki gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar dattawan Arewa, ta yi Allah wadai da ci gaba da tsare tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf.
Ƙungiyar ta bayyana kamun da EFCC ta yi wa Farfesa Usman Yusuf, a matsayin wani yunƙuri na murkushe masu sukar gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Tinubu.
Dattawan na Arewa sun buƙaci da a gaggauta sakin tsohon shugaban na hukumar NHIS ba tare da ɓata lokaci ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
