Bayan Raba Tallafin Awaki, Gwamna Abba Ya Ware Biliyoyi don Auren Gata a Kano

Bayan Raba Tallafin Awaki, Gwamna Abba Ya Ware Biliyoyi don Auren Gata a Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta yi ƙarin haske kan abin da kasafin kuɗin shekarar 2025 ya ƙunsa
  • Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kuɗi ya bayyana cewa daga cikin kuɗaɗen da aka ware har da na shirya bukukuwan aure
  • Musa Shanono ya bayyana cewa kasafin kuɗin na shekarar 2025 da majalisa ta amince da shi ya fi na shekarar 2024 da N282.41bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware biliyoyin kuɗi domin shirya bikin aure.

Gwamnatin ta ware N2.5bn domin gudanar da bukukuwan aure a cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar a shekarar 2025.

Gwamna Abba zai yi auren gata
Gwamnatin Kano za ta yi auren gata Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kuɗi na jihar, Musa Shanono, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Hajjin 2025: Gwamna Radda ya gano hanyar saukakawa maniyyata kashe kudi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da kasafin kuɗin Kano ya ƙunsa

Musa Shanono ya yi bayani kan abin da kasafin kuɗin na 2025 wanda majalisar dokokin jihar ta amince da shi ya ƙunsa, rahoton Daily Post ya tabbatar.

A cewarsa, gwamnati ta shirya kashe N91.32bn a fannin gudanar da mulki da samar da ingantattun ayyuka, wanda ciki har da shirya bukukuwan aure.

Ya ce wannan ƙudiri yana da nufin ƙarfafa shugabanci, kare haƙƙin bil’adama, tare da ƙarfafa adalci domin ci gaban al’umma mai dorewa da kuma kyautata rayuwar jama'a.

Musa Shanono ya bayyana cewa daga cikin adadin da aka ware, an tanadi N1bn domin rabon abinci a lokacin azumin Ramadan.

Sannan an ware N955m domin gudanar da bincike kan ƙididdigar ma’aikata, binciken yanayin gidaje, da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Haka nan kuma, an ware N1.049bn domin siyan na'urorin gurzo takardu, gyaran tsarin samar da ruwa, da kuma siyan kayan aiki na ɗakin karatu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto ya mika bukatarsa ga shugabannin tsaro kan 'yan bindiga

Ya kuma ƙara da cewa an tanadi N267.6m domin samar da kayayyakin more rayuwa da kuma tallafawa aikin Da'awa tare da buga kalandar Musulunci da tallafawa sababbin shiga Musulunci.

Sauran abubuwan da aka ware kuɗi domin su sun haɗa da N589m don gudanar da bincike kan tsaro da ba da tallafi, tare da dakile bara a tituna.

An kuma ware N200m domin siyan kujeru da kayayyakin aiki na ofishin Akanta Janar, gyare-gyare, da sauran abubuwa.

Kasafin kuɗin 2025 ya fi na 2024

Kwamishinan ya bayyana cewa jimillar kasafin kuɗin da aka amince da shi na 2025 ya kai N719.75bn, wanda hakan ke nuna samun ƙarin N170.59bn ko kaso 31%, fiye da asalin kasafin N549.16bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar.

Ya bayyana cewa za a kashe jimillar kuɗi N262.67bn kan abubuwan yau da kullum, yayin da aka ware N457.08bm kan ayyukan ci gaba.

Kasafin kuɗin na shekarar 2025 ya fi na 2024 da N282.41bn, wanda hakan ke nuna samun ƙaruwar kaso 65%.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta

Ba abin da ake buƙata ba kenan

Ibrahim Zulkiful Saleh ya bayyanawa Legit Hausa cewa auren gata ba abin da ake buƙata ba ne a jihar Kano, duba da irin tarin matsalolin da suka addabi jihar.

"Gaskiya bai kamata a ware waɗannan maƙudan kuɗaɗen ba domin gudanar da wani auren gata. Akwai tarin matsalolin da sukaa addabi Kano da ya kamata a ce an maida hankali a kansu."
"Duk wanda yake son aure ya je ya yi da kuɗinsa, ba wai gwamnati ta ware kuɗaɗe domin yi wa mutane aure ba."

-.Ibrahim Zulkiful Saleh

Gwamna Abba ya ƙudiri aniyar yaƙar rashawa

A wani labarin kuma, kun ji gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna cewa gwamnatinsa ba za ta yarda da cin hanci da rashawa ba.

Gwamna Abba lashi takobin yin yaƙi da cin hanci da rashawa, zalunci da danniya a jihar Kano domin samun ci gaba mai ɗorewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng