Halin da aka Shiga bayan an Bukaci a Sauke Sufeton 'Yan Sandan Najeriya
- Ce-ce-ku-ce ya sake kunno kai kan tsawaita wa’adin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun
- Tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore na cikin wadanda suke ganin tsawaita wa’adin Sufeton ba bisa ka'ida yake ba
- Yayin da yan Najeriya ke magana kan lamarin, gwamnatin tarayya ta ce an kara wa'adin nada Egbetokun ne bisa dokar kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ana ci gaba da takaddama kan tsawaita wa’adin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Kayode Egbetokun, bayan wasu manyan ‘yan gwagwarmaya sun nemi a tsige shi.
Daya daga cikin manyan masu sukar lamarin shi ne Omoyele Sowore, wanda ke ci gaba da kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tsige Egbetokun.

Asali: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta yi magana cewa an kara wa sufeton wa'adi kuma hakan bai saba doka ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan Shari’a ya ce majalisa ta yi wa dokar ‘yan sanda gyara kafin wa’adin sufeton ya kare wanda hakan ya ba shi damar cigaba da aiki.
Sowore ya kalubalanci wa'adin shugaban ƴan sanda
Omoyele Sowore da ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar AAC a zaben da ya gabata, ya ce zai ci gaba da kalubalantar rike mukamin IGP da Egbetokun ke yi.
Dan gwagwarmayar ya ce hakan ya zama dole lura da cewa an tsawaita wa’adinsa ba bisa ka’ida ba.
Wannan rikicin ya barke ne a ranar Litinin bayan da jami’an ‘yan sanda suka gayyaci Sowore don yi masa tambayoyi kan kalaman da ya yi, kafin daga bisani suka tsare shi.
Lamarin ya cigaba a daukar hankalin 'yan Najeriya musamman a kafafen sada zumunta, wanda hakan ke kara rura wuta da jawo ce-ce-ku-ce.
An gyara dokar 'yan sandan Najeriya
Rahotanni sun nuna cewa, tun a watan Satumba na shekarar 2024 ne Egbetokun ya cika shekaru 60 da haihuwa, wanda hakan ke nuna cewa ya kamata ya yi ritaya daga aiki.
Sai dai, shugaba Bola Tinubu ya tsawaita wa’adinsa na shekara hudu bayan Majalisar Dokoki ta kasa ta gaggauta gyara dokar ‘yan sanda a watan Yuli na 2024.
Gayaran dokar na nuni da cewa Sufeto Janar yana da cikakken wa’adi na shekaru hudu ko da shekarunsa na ritaya sun yi.
Gwamnati ta kare kara wa’adin IGP
Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya bayyana cewa an nada Egbetokun ne bisa doka, kuma babu wani abu da ya saba wa tsarin mulki a tsawaita wa’adinsa.
Rundunar 'yan sanda ta wallafa a Facebook cewa ministan shari'ar ya ce:
"Wa’adin Egbetokun wanda ya fara daga ranar 31 ga watan Oktoba, 2023, zai ci gaba har zuwa ƙarshen wa’adin shekaru hudu da aka tanada a doka."

Kara karanta wannan
Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT
Ya kara da cewa kafin wa’adinsa ya kare a shekarar 2024, an riga an yi gyaran doka domin bai wa IGP damar kammala cikakken wa’adin aikinsa.
Sai dai duk da karin bayanin, ana cigaba da magana a kafafen sada zumunta inda 'yan Najeriya ke cigaba da cewa an yi rufa rufa wajen karawa sufeton wa'adi.
Martanin Atiku kan kama Sowore
A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubakar ya kalubalanci kama dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da 'yan sanda suka yi.
Legit ta rahoto cewa Atiku ya ce kama Sowore da Farfesa Usman Yusuf na cikin matakan gwamnati na toshe muryoyin 'yan adawa a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng