"Gwamnatinmu ba za Ta Raga ba," Abba Gida Gida Ya Zare Takobin Yaki da Rashawa

"Gwamnatinmu ba za Ta Raga ba," Abba Gida Gida Ya Zare Takobin Yaki da Rashawa

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa jama'ar da su ka zabe shi cewa ya na a kan bakarsa na yaki da rashawa, zalunci da danniya
  • A matsayin godiya bisa kammala hanyar Fulatan-Zarewa-Danguzuri, al’ummar Rogo sun ba wa gwamna kyautar takobi da kuma Alƙur’an
  • Mai girma Abba Kabir ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da muhimman ayyukan da ke inganta rayuwar al’ummar jihar Kano

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na yaki da rashawa, zalunci, da danniya a jihar.

Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da titin da aka gina mai tsawon kilomita tara, wanda ke hada garuruwan Fulatan, Zarewa, da Danguzuri a Karamar Hukumar Rogo.

Kara karanta wannan

Jikin tsohon gwamnan Taraba ya rikice, kotu ta ba shi damar neman lafiya, an tono barnarsa

Kwankwasiyya
Abba ya lashi takobin yaki da rashawa Hoto: Kwankwasiyya reporters
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Daraktan Yada Labaran Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce Abba Kabir Yusuf ya zare takobin yaki da azzalumai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Ishaq Falalu Zarewa ne ya mika wa gwamnan Kanio takobin a madadin mazauna yankunan da aka gudanar da aikin.

‘Yan Kano sun yi wa gwamna Abba kyauta

Kwankwasiyya reporters ta wallafa cewa mutanen Karamar Hukumar Rogo sun bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kyautar takobi da Alƙur’ani mai tsarki da aka rubuta da hannu.

Sun ce wannan kyauta alama ce ta godiya bisa kokarin da gwamnatinsa ta yi wajen kammala wannan muhimmiyar hanya da za ta habaka tattalin arziki da saukaka rayuwar al’umma.

Abba ya dauki alkawarin yaki da rashawa

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci rashawa, danniya, ko zalunci ba, yana mai tabbatar da cewa ba za a hana ci gaban Kano ba.

Ya yi alkawarin ci gaba da inganta ababen more rayuwa, karfafa ci gaban tattalin arziki, da tabbatar da cewa gwamnati na aiki don amfanin al’umma.

Kara karanta wannan

Yaki da talauci: Gwamnan Jigawa ya raba tallafin kudi ta katin ATM

Ya ce:

“Ina so al’ummar Kano su sani cewa wannan hanya shaida ce ta jajircewarmu wajen bunkasa kasuwanci da noma a wannan yanki. Za mu ci gaba da ba da fifiko ga manyan ayyuka da ke inganta rayuwar al’umma.”

Abba ya nanata matsayar gwamnatinsa

Wannan shi ne karo na uku da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke nuna shirin gwamnatinsa na fuskantar duk wata barazana da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban Kano.

Ya bukaci al’umma da su ci gaba da goyon bayan kyakkyawan shugabanci, yana mai alkawarin yin aiki tukuru don tabbatar da cewa Kano ta zarce matsayin da take kafin shekarar 2023.

An kama hadimin Abba Gida Gida

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan kasar nan, reshen jihar Kano ta cafke daya daga cikin hadiman Gwamna Abba Kabir Yusuf, Abba Zizu bisa zargin cin zarafi.

Kara karanta wannan

Abincin wasu ya kare: Gwamna ya fatattaki kwamishinoni 5, an maye gurbinsu nan take

A cewar takardar koke da lauya Hussain Maqari ya shigar gaban AIG Zone 1, wanda aka ci zarafin, Mahbub Hassan, na aiki a ma’aikatar noma, ana zargin ya hana wani bako ganin kwamishina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel