Tankar Fetur Ta Yi Bindiga a Gidan Mai a Jigawa, Ta Tayar da Gobara
- Rahotanni na nuni da cewa gobara ta tashi a gidan man Shakkato da ke kan hanayar Kiyawa a Dutse na jihar Jigawa yayin da ake sauke fetur daga cikin tanka
- An ruwaito cewa hukumar kashe gobara da jami’an tsaro sun dakile gobarar tare da kare dukiya da rayukan al'ummar da ke yankin
- Haka zalika, rahoton 'yan sanda ya nuna cewa a yanzu haka ba a fitar da adadin asarar da wutar ta jawo ba, kuma ana tattara bayanai kan hadarin
- Wani shaidar gani da ido, Kamalu Musa ya yi wa Legit karin haske kan halin da aka shiga yayin faruwar hadarin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Gobara ta tashi a gidan man Shakkato da ke kan titin Kiyawa a birnin Dutse, jihar Jigawa, kuma ta jawo asarar dukiya mai yawa.
Bisa bayanan da ‘yan sanda suka fitar, gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 7:00 na yamma ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu, 2025.

Asali: Getty Images
Kakakin 'yan sandan jihar Jigawa, SP Shiisu Adam Lawal ne tabbatar wa Legit faruwar gobarar da kuma matakin da jami'an tsaro suka dauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba ko kuma wani mutum da ya jikkata sakamakon tashin wutar.
Yadda gobara ta tashi a gidan man Jigawa
Binciken farko da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa gobarar ta tashi ne yayin da ake sauke mai daga tankar man fetur zuwa rijiyar ajiya.
A cewar sanarwar 'yan sanda, wutar ta tashi kwatsam, sannan ta ci gaba da bazuwa cikin gidan man, abin da ya sa ma’aikatan wajen suka gagara shawo kanta.
A sakamakon haka ne jami’an tsaro da hukumar kashe gobara ta jihar da ta tarayya suka hanzarta zuwa wurin domin hana cigaban bazuwar gobarar.

Kara karanta wannan
Majalisar dokokin Kano ta fusata bayan gano abin da ake yi a gidajen da Kwankwaso ya gina
Matakin da 'yan sanda suka dauka
Daga samun rahoton faruwar gobarar, rundunar ‘yan sandan Dutse ƙarƙashin jagorancin DPO na yankin ta gaggauta kai ɗauki.
Haka kuma, jami’an hukumar kashe gobara ta jihar da ta tarayya sun isa wurin tare da jami’an tsaro domin shawo kan lamarin.
Tare da haɗin gwiwar mutanen gari, an yi nasarar kashe gobarar, yayin da ‘yan sanda suka killace wurin domin hana barayi yin amfani da wannan dama su yi sata.
An yi asarar rai a gobarar Jigawa?
Duk da cewa ba a samu asarar rai ko raunuka ba, har yanzu ba a tantance yawan dukiyar da gobarar ta lalata ba.
Hukumar kashe gobara da hukumomin da abin ya shafa na ci gaba da gudanar da bincike domin tantance yawan asarar da aka yi.
A halin yanzu, harkoki sun dawo daidai, kuma ana cigaba da harkoki a kan titin Kiyawa da ke kusa da gidan man ba tare da wata tangarda ba.
A 'yan kwanakin nan ana cigaba da samun gobara a sanadiyyar fashewar tankar man fetur a jihohin Najeriya.
Legit ta tattauna da Kamalu Musa
Wani mazaunin Duste, Kamalu Musa da ya ce hadarin ya faru a lokacin da yake hanyar komawa gida daga wajen aiki ya ce ba a samu wadanda suka yi kokarin dibar fetur ba.
"Mutane ba su je diban fetur ba, zai iya yiwuwa hakan na da alaka da ganin wuta ta fara ci sosai bayan da abi ya faru.
"Wata kila da wutar ba ta kama da wuri ba a samu masu zuwa diban fetur."
- Kamalu Musa
An raba tallafin kudi ta ATM a Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa ya raba tallafin kudi ga al'umma ta katin ATM a dukkan kananan hukumomi.
Gwamnatin jihar ta ce mutane 23,000 ne za su amfana da shirin domin rage musu radadin tsadar rayuwa da mastin tattalin arziki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng