'Qur'anic Festival': Bala Lau Ya Yi Raddi ga Sheikh Jingir, Ya Tuno Rashin Mutunci da Ya Yi Masa
- Abdullahi Bala Lau ya yi martani ga shugaban Izalah ta Jos, Sani Yahaya Jingir, yana mai bayyana yadda dattijon ke nisantar duk wani taronsu
- Malamin ya ce abin takaici ne yadda Sheikh Jingir ke yin fatali da kowanne alheri da ke fitowa daga bangarensu ba tare da dalili ba
- Ya bayyana cewa wata mata ta so taimakawa wajen kammala masallaci ta hannunsa, amma Sheikh Jingir ya ki amincewa da hakan
- Sheikh Bala Lau ya yi kira ga sauran mabiya Ahlus Sunnah su goyi bayan wannan shiri, yana mai cewa a shirye suke su karbi gyara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kungiyar Izalah bangaren Kaduna ya yi martani ga Sheikh Sani Yahaya Jingir kan 'Qur'anic Festival' da ake ta ce-ce-ku-ce a kai a kwanakin nan.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya koka kan halayen dattijon inda ya ce duk inda suke ko suna shirin aikin alheri bai son zuwa wurin saboda son rai da yake da shi.

Asali: Facebook
Sheikh Bala Lau ya soki Sheikh Yahaya Jingir
Sheikh Bala Lau ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Talata 28 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya ce abin takaici ne yadda Yahaya Jingir ke gudun duk wani alheri da zai fito daga ɓangarensu ko da kuwa zai kawo wa Musulunci ci gaba.
Shehin malamin ya bayyana yadda ya yi niyyar yin abin alheri ga bangarensu amma Sheikh Jingir ya yi fatali da shi.
Halayen Yahaya Jingir da Bala Lau ya jero
"Ba alfahari ba, duk abin da aka ce muna ciki, shi wannan dattijo ko tsohon ba zai shiga ciki ba.
"Ina son in fada muku, komai alherin abin ba zai shiga ba, saboda ya saba zage-zage da fadin maganganu a kanmu.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
"Duk lokacin da ya fadi maganan ko cin mutuncin ni abin da nake dauka bayansa kawai daukaka Allah yake kawo mana."
- Sheikh Abdullahi Bala Lau
Bala Lau ya yi kira ga sauran 'Ahlus Sunnah'
Sheikh Bala Lau ya bayyana yadda wata mata ta yi niyyar karisa musu masallaci ta hannunsa amma Sheikh Jingir ya ki amincewa saboda alherin daga gare shi ne.
Malamin ya ce hakan abin takaici ne wanda ya kamata su hada kai wurin tabbatar da ci gaban Musulunci ba tare da nuna wani bambanci a tsakani ba.
Shehin malamin ya yi kira da sauran 'Ahlus Sunnah' da su goyi bayan wannan shiri inda ya ce a shirye suke domin karbar gyararraki.
Majalisar Musulunci ta magantu kan 'Quranic Festival'
Kun ji cewa Majalisar Kolin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta bayyana goyon bayanta ga taron 'Qur’anic Festival' da aka shirya gudanarwa a birnin Abuja.
Sakataren Majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede ya ce an shirya taron ne don haɗa kan Musulmin Najeriya da nuna baiwar ilimin Alkur’ani ba kamar yadda ake zargi ba.
Ya kara da bayyana yadda aka samo tunanin shirya taron, wanda tuni ya fara yamutsa hazo a tsakanin Musulmin Najeriya da wasu ke zargin akwai siyasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng