Bayan an Nemi Ya Fice daga PDP, Gwamna Ya Ɗauko Mutum 8 Ya ba Su Muƙamai

Bayan an Nemi Ya Fice daga PDP, Gwamna Ya Ɗauko Mutum 8 Ya ba Su Muƙamai

  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya naɗa sababbin masu ba shi shawara ta musamman guda takwas domin karfafa gwamnatinsa
  • Sanata Bala Ƙauran Bauchi ya shirya rantsar da su tare da wasu mutum uku da ya naɗa a kwanakin baya a fadar gwamnati ranar Talata
  • Mai magana da yawun gwamnan ya ce Bala Mohammed ya yi wa ƙabilu da addinai adalci a wannan sababbin naɗe-naɗe da ya yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya amince da nadin ƙarin hadimai masu ba shi shawara guda takwas.

Gwamna Bala, shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP ya naɗa sababbin hadiman ne domin karfafa gwamnatinsa wajen a aiwatar da shirye-shiryen ci gaba.

Gwamna Bala Mohammed.
Gwamnan Bauchi ya nada sababbin masu ba shi shawara guda takwas Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Facebook

Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin watsa labarai da hulɗa da jama’a, Kwamared Mukhtar Gidado, ne bayyana hakan a sanarwa, Tribune Nigeria ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan da gwamna ya yi la'akari da su

Ya ce gwamnan ya yi la'akari da banbancin ƙabilu da addinai wajen yin sababbin naɗe-naɗen ta yadda babu wanda zai koka kan rashin adalci.

Kakakin gwamnan ya ce hakan ya kara tabbatar da kudirin Bala Mohammed na tabbatar da shugabanci na gari, hadin kai, da kuma kawo sauye-sauye masu tasiri ga rayuwar al’umma.

Bugu da ƙari, sanarwar ta ce gwamnan ya naɗa mutane takwas ne bayan la'akari da gogewa da jajircewarsu, wanda zai taimakawa gwamnatinsa ta cika alƙawurra.

Jerin sababbin hadiman gwamnan Bauchi

Sababbin masu ba gwamnan shawara sun hada da:

1. Hon. Sanusi Khalifa (Toro) – Mai bai wa gwamna shawara kan kan harkokin ma'adanai.

2. Hon. Haladu Ayuba (Dambam) – Mai ba gwamna shawara kan inganta rayuwa.

3. Hon. Jidauna Tula (Bogoro) – Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin shari’a.

4. Hon. Adamu Bello (Giade) – Mai bai wa gwamna shawara kan viniki da masana’antu.

Kara karanta wannan

Mazauna Jigawa za su fara ganawa da gwamnansu kai tsaye

5. Alhaji Danladi Mohammed Danbaba (Bauchi) – Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin jin ƙai.

6. Hon. Sani Mohammed Burra (Ningi) – Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin majalisar jiha/ƙasa.

7. Hon. Yakub Ibrahim Hamza (Darazo) – Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin ilimin gaba da sakandare.

8. Hon. Shitu Zaki (Zaki) – Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin siyasa.

Yaushe gwamna zai rantsar da su?

Wadannan hadimai guda takwas, tare da guda uku da aka nada a baya, za a rantsar da su ranar Talata, 28 ga Janairu 2025 a gidan gwamnatin Bauchi da karfe 12:00 rana.

Gwamna Bala Mohammed ya taya wadanda aka nada murna tare da bukatar su nuna jajircewa, gaskiya, da ƙwarin gwiwa wajen yi wa al’ummar jihar Bauchi hidima.

Gwamna Bala ya faɗi dalilin korar kwamishinoni

A wani labarin, an ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya yi ƙarin haske kan korar da ya yi wa wasu kwamishinoni a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Buhari, Radda da manyan 'yan siyasa sun yi taron neman nasara ga APC

Gwamnan ya ce ba wai don rashin gaskiya ko wani laifi ne ya sa ya sallami kwamishinonin ba, ya ɗauki matakkin ne domin sa kowa a gurbin da ya dace.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel