'Yan Sanda Sun Yi Magana kan Cafke Muhuyi Magaji, Sun Fadi Abin da Ya Faru
- Rundunar ƴan sandan Najeriya ta fito ta yi ƙarin haske kan zargin da Muhuyi Magaji ya yi na cewa jami'anta sun cafkse shi
- Kakakin rundunar ƴan sandan a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa gayyatar shugaban na hukumar PCACC aka yi, ba cafke shi ba
- ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana cewa an gayyaci Muhuyi Magaji ne bayan da aka shigar da wani ƙarafi a kansa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta yi magana kan batun cafke shugaban hukumar kula da ƙorafe-ƙorafen jama'a da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimingado.
Rundunar ƴan sandan ta musanta cewa ta cafke shugaban hukumar ta PCACC mai yaƙi da cin hanci a jihar Kano.

Source: Facebook
Ƴan sanda sun taɓo batun cafke Muhuyi Magaji
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a shafin X na rundunar.
Kakakin ƴan sandan yayin da yake martani kan zargin da Muhuyi Magaji ya yi na cewa an cafke shi, ya ce ko kaɗan ba haka abin yake ba.
ACP Olumiyiwa Adejobi ya bayyana gayyatar Muhuyi Magaji aka yi sakamakon wani ƙorafi da aka shigar a kansa.
Ƴan sanda sun musanta cafke Muhuyi Magaji
Ya ƙara da cewa duk maganar da ke nuna cewa cafke Muhuyi Magaji aka yi, babu ƙamshin gaskiya a cikinta.
"Ƴan sanda sun lura da kalaman da shugaban hukumar PCACC, Muhuyi Magaji, ya yi kan zargin ƴan sanda sun cafke shi."
"Muna so mu fayyace cewa ba cafke Muhuyi Magaji aka yi ba, a maimakon hakan rundunar ƴan sanda ta gayyace shi ne sakamakon wani ƙorafi da aka shigar a kansa."
"A ranar Juma'a, 17 ga watan Janairun 2025, mataimakin sufeton ƴan sanda ya karɓi ƙorafi a kan Muhuyi. Bisa tsari da ƙa'idojin bincike, an gayyace shi domin ya tattauna da jami'ai domin gano bakin zaren matsalar."

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta
"Duba da rawar da yake takawa a matsayinsa na jami'in gwamnati kuma wanda ake ganin girmansa a cikin al'umma, ya kamata Muhuyi ya ba ƴan sanda haɗin kai domin gudanar da cikakken bincike, maimakon jawo surutu a kafafen yaɗa labarai."
"Duk wata magana da ke nuna cewa an cafke Muhuyi Magaji babu ƙamshin gaskiya a cikinta. Muna kira ga kafafen yaɗa labarai da sauran jama'a da su guji yaɗa ƙaryar da za ta iya kawo hayaniya ko ruɗani."
"Rundunar ƴan sanda a jajirce take wajen bin doka da oda a dukkanin binciken da take yi."
- ACP Olumuyiwa Adejobi
Muhuyi Magaji ya magantu kan cafke shi
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar kula da ƙorafe-ƙorafen jama'a da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimingado, ya yi magana kan kamun da ƴan sanda suka yi masa.
Shugaban na hukumar PCACC ya bayyana cewa ƴan sanda sun cafke shi ne saboda binciken da yake yi a badaƙalar karkatar da kuɗaɗe a kamfanin KASCO.
Asali: Legit.ng
