Wani Katafaren Otal da Kamfanoni 4 Sun Shiga Gonar Gwamnatin Kano, An Ɗauki Mataki
- Gwamnatin jihar Kano ta hannun hukumar tara haraji ta jiha watau KIRS ta rufe kamfanoni da otal kan rashin biyan kuɗin haraji yadda ya kamata
- Daraktan gudanarwa na sashin kula da basussuka, Malam Ibrahim Abdullahi ya ce wannan mataki ya zama dole saboda yadda kamfanonin suka raina gwamnati
- Hukumar KIRS ta bayyana cewa za ta ci gaba da aiki tuƙuru domin samar da ƙarin kuɗaɗen shiga ga gwamnatin jihar Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano karƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta fara ɗaukar matakai masu tsauri kan kamfanonin da suke wasa da biyan haraji.
Hukumar tara haraji ta jihar Kano (KIRS) ta kulle wani otal da wasu kamfanoni guda huɗu saboda gazawar su wajen biyan haraji.

Source: Facebook
Daily Trust ta ce a madadin gwamnatin Kano, hukumar KIRS ta rufe kamfanonin saboda sun ƙi biyan harajin Pay As You Earn (PAYE) da sauran basussukan haraji da suka taru a kansu.

Kara karanta wannan
Kudiri yayi nisa a majalisa, Gwamna Abba zai kafa hukumar tsaro mallakin jihar Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Otal da kamfanoni 4 da aka rufe
Kamfanonin da aka rufe sun haɗa da katafaren otal na Grand Central, Nikita Textile Limited, Fursa Foods Limited, Next Door, da SKY, kamar yadda hukumar ta bayyana.
A cewar shugaban tawagar aiwatar da wannan mataki, daraktan gudanarwa da basussuka na hukumar FIRS, Malam Ibrahim Abdullahi, wannan matakin ya zama dole.
Ya ce gwamnati ta kulle kamfanonin ne bayan tunatar da su kuɗin harajin da ake binsu bashi amma suka sa ƙafa suka shure.
Gwamnatin Kano ta bi doka kafin rufe su
Saboda haka, hukumar ta nemi izinin kotu don kulle wuraren kasuwancin waɗannan kamfanonin a matsayin wata hanya ta tabbatar da bin dokar biyan haraji a kan lokaci.
Malam Ibrahim ya ce:
“An kulle otal na Grand Central Hotel saboda rashin biyan haraji da ya haura Naira miliyan 14.Mun kulle kamfanin Nikita Textile saboda rashin biyan harajin da ya kai fiye da naira miliyan 229.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
"Mun karɓe sauran kamfanonin saboda gazawar su wajen biyan harajin da ya kamata su biya ga gwamnatin jihar.”
Hukumar KIRS ta tashi tsaye kan haraji
Daraktan ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da cewa duk wata hanyar da ke kawo hasarar kudaden shiga ga jihar an toshe ta.
Ya bayyana cewa duk wani kamfani da aka kulle ba za a buɗe shi ba har ya biya dukkan basussukan da ake binsa.
Ya jaddada cewa matakin wani ɓangare ne na yunƙurin hukumar na tabbatar da karuwar kudaden shiga ga jihar Kano ta hanyar bin diddigin haraji daga ƴan kasuwanci.
PCACC ta ce shari'ar Ganduje ba fashi
A wani labarin, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ba gudu ba ja da baya a shari'ar da take da tsohon gwamna kuma shigaban APC, Abdullahi Ganduje.
Hukumar PCACC ta nanata kudirinta na ci gaba da shari'ar Ganduje ne bayan wasu rahotanni sun nuna cewa ƴan sanda sun kama shugabanta. Muhuyi Magaji.
Asali: Legit.ng