Rigima Ta Ɓarke a Babban Masallaci kan Limanci, Gwamnati Ta Hana Sallah a Wurin
- Rigima ta kaure kan limanci a wani masallaci da ke yankin ƙaramar hukumar Agege a jihar Legas bayan rasuwar babban liman, Malam Habib
- Shugaban ƙaramar hukumar Agege, Ganiyu Egunjobi ya ba da umarnin rufe masallacin nan take domin gudun tashin-tashina a yankin
- Ya ce za a shirya zama da dukkan ɓangarorin biyu domin lalubo mafita da kuma magance yiwuwar tada zaune tsay ƙafin sake buɗe masallacin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Lagos - An rufe wani babban masallaci mai suna 'Mosalasi Alhaja' da ke karamar kukumar Agege ta jihar Legas sakamakon rikicin shugabanci.
Rikicin limancin ya ɓare a babban masallacin ne biyo bayan rasuwar babban limamin al'ummar, Malam Habib Abdulmajid.

Asali: Original
An hana Sallah a masallacin na wucin gadi
Shugaban karamar hukumar Agege, Ganiyu Egunjobi, ne ya sanar da matakin rufe masallacin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Premium Times ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan matakin ya biyo bayan takaddama tsakanin iyalan marigayi limamin da mataimakinsa, Mustapha Muktar, dangane da wanda ya kamata ya jagoranci masallacin.
Ciyaman na Agege ya ce an rufe masallacin domin daƙile yiwuwar ɓarkewar rikici a cikin al’umma, musamman a tsakanin Hausawa da ke zaune a yankin.
“Dole ne a dauki wannan matakin domin tabbatar da tsaron lafiyar jama’a da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin Agege.
"Sabani irin wannan kan iya rikidewa zuwa rikici mai muni idan ba a dauki matakin da ya dace ba,” in ji Egunjobi.
Shugaban Agege ya ziyarci masallacin
Shugaban karamar hukumar ya ce gwamnatinsa ba za ta zuba ido ta bar duk wani abu da ka iya tayar da zaune tsaye ba a yankin Agege.
Ganiyu Egunjobi ya bayyana cewa matakin rufe masallacin zai fara aiki ne nan take, ba tare da wani ɓata lokaci ba, kamar yadda The Nation ta kawo.
Hakazalika, ya tabbatar wa da jama’a cewa za a samar da isasshen tsaro a yankin domin hana duk wani tashin hankali da ka iya biyo baya.
Bugu da ƙari, Egunjobi ya ziyarci masallacin tare da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa an aiwatar da umarninsa.
Za a shirya zaman sulhu
Hon. Egunjobi ya kuma sanar da cewa za a shirya taron masu ruwa da tsaki, inda za a gayyaci dukkan bangarorin da ke rikici domin tattauna matsalar shugabanci tare da nemo mafita mai dorewa.
A cewarsa, ya yi haka ne da nufin dawo da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’umma, tare da tabbatar da cewa masallacin ya ci gaba da kasancewa wuri na ibada da kuma zaman lafiya ga kowa.
Wannan rikici ya ja hankalin al’umma da dama, musamman Hausawa, waɗanda ke fatan a warware shi cikin lumana.
Limamin Juma'a ya yi wa Bola Tinubu nasiha

Kara karanta wannan
Cire tallafin fetur: Mataimakin shugaban majalisa ya fadi alherin da Najeriya ta samu
A wani labarin, kun ji cewa limamin masallacin Juma'a a jihar Legas ya yi wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu nasiha kan shugabanci.
Babban limamin masallacin Lekki, Sheikh Jamiu ya yi addu’a ga shugaba Tinubu domin samun nasara wajen jagorantar Najeriya zuwa tudun mun tsira.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng