'Yan Bindiga Sun Shiga Kano, Sun Sace Diyar Babban Attajirin Dan Kasuwa
- Ƴan bindiga sun kai hari a garin Garo a ƙaramar hukumar Kabo ta jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Miyagun ƴan bindigan a yayin harin da suka kai sun yi garkuwa da ɗiyar wani attajirin ɗan kasuwa bayan sun karɓi N8m
- Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce an tura jami'ai domin zaƙulo waɗanda suka kai harin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki gidan wani attajirin ɗan kasuwan mai suna Alhaji Auwal a garin Garo, ƙaramar hukumar Kabo ta jihar Kano.
Ƴan bindigan sun yi garkuwa da ɗiyar ɗan kasuwan, mai suna Zainab, bayan sun karɓi Naira miliyan 8 daga iyalanta.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa lamarin ya auku ne da safiyar ranar Lahadi, 26 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka sace ɗiyar attajiri
An tattaro cewa mummunan lamarin ya auku ne lokacin da maharan, su kimanin mutum 10, suka kutsa gidan sanannen ɗan kasuwar, Alhaji Auwal.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa maharan sun kutsa gidan ne bayan sun ƙarya ƙofar shiga gidan da ƙarfin tsiya.
"Mutum uku daga cikinsu suna ɗauke da bindigogi, yayin da sauran mutum bakwai suka riƙe wasu makamai daban-daban."
“Sun tattara dukkan iyalin a wuri guda, sannan suka riƙa abubuwan da suka tayar da hankulan mutanen tare da firgita su."
"Mai gidan ya roƙe su da ka da su taɓa iyalinsa, inda ya ba su tabbacin zai cika dukkan buƙatunsu don tabbatar da lafiyarsu. Sai ƴan bindigan suka buƙaci a ba su kuɗi, sai aka ba su Naira miliyan takwas."
“Duk da haka, bayan sun karɓi kuɗin, sai suka yi garkuwa da babbar ɗiyar mai gidan, wata yarinya wacce ta kammala makarantar sakandare, kafin su tsere."

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta
- Wata majiya
Ba a san inda aka kai yarinyar ba, saboda masu garkuwa da mutanen ba su tuntuɓi iyayenta ba har yanzu.
Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Kano
Lamarin ya faru ne kimanin awanni 48 bayan ƴan bindiga sun kashe wani tsohon babban sakatare a jihar Gombe kuma tsohon shugaban hukumar tara haraji ta jihar Gombe, Atiku Mu’azu.
Marigayin dai an kashe shi ne bayan an yi garkuwa da shi a gidansa da ke Janbulo, Kano, bayan karɓar Naira miliyan 10.
Wannan lamarin dai ya jefa al’umma cikin firgici da tsananin tashin hankali.
Ƴan sanda sun tabbatar da harin
Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Kakakin ƴan sanda ya bayyana cewa tawagar jami'an tsaro domin ceto yarinyar tare da cafke miyagun da suka sace ta.
"An tura tawagar jami'an yaƙi da garkuwa da mutane domin ceto yarinyar tare da cafke waɗanda suka aikata laifin."
- SP Abdullahi Haruna Kiyawa
Ƴan bindiga sun buƙaci kuɗin fansa
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindigan da suka sace ma'aikatan lafiya a jihar Katsina, sun buƙaci a ba su maƙudan kuɗaɗen fansa.
Ƴan bindigan sun buƙaci a ba su N540m a matsayin kuɗaɗen fansa kafin su sako mutanen waɗanda suka yi garkuwa da su a asibitin Kankara.
Asali: Legit.ng