"Na Kusa Cika Alkawurran da na Yi wa Talakawa," Gwamna Ya Haska Abubuwan da Ya Yi
- Mai girma gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu ya ce ya cika kaso 70 cikin 100 na alkawrurran da ya yi wa talakawa a lokacin kamfe
- Gwamna Nasir ya bayyana haka ne da ya karbi bakuncin deleget na APC waɗanda suka zaɓe shi a lokacin zaben fidda gwani a 2022
- Kauran Gwandu ya ce gwamnatinsa ta fita daban da sauran jihohin wajen shekarun da ma'aikacin gwamnati zai ɗauka a bakin aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya yi ikirarin cewa ya cika sama da kashi 70 cikin 100 na alkawurran da ya dauka a yakin neman zabensa a 2023.
Gwamna Nasir Ƙauran Gwandu ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da wakilan APC waɗanda suka zaɓe shi a zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna a 2022.

Asali: Facebook
Nasir Idris ya godewa deleget na APC da suka kaɗa masa kuri'u har ya zama ɗan takara kuma ya ci zaɓen 2023, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Kebbi ya kusa gama cika alƙawurra
Gwamnan ya tabbatar wa deleget cewa kuri’unsu ba su tafi a banza ba, yana mai jaddada cewa an samu gagarumin ci gaba a jihar karkashin jagorancinsa.
Ya ƙara gode musu bisa cikakken goyon bayansu da hangen nesan da suka yi wajen zabar sa a matsayin dan takarar APC domin kayar da jam’iyyun adawa a 2023.
"Abin da na sani a yau shi ne, ina alfahari da farin cikin sanar da ku cewa na cika sama da kashi 70 cikin 100 na alkawurran kamfe da na dauka a gaban al’umma lokacin da kuka zabe ni a matsayin gwamna a 2023.
“Idan kun zagaya babban birnin jihar, Birnin Kebbi, da sauran manyan kananan hukumomi na Kebbi, za ku ga gagarumin ci gaban da aka samu, don haka kuri’unku ba su tafi a banza ba da kuma zaɓe ni,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
Gwamnatin Kebbi ta kara shekarun aiki
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa ta kara shekarun ritayar malamai zuwa shekaru 65 ko shekara 40 a bakin aiki.
Dr. Nasir Idris ya ce wannan doka kaɗai ta bambanta jihar Kebbi da sauran jihohin Najeriya.
Har ila yau, ya ce gwamnatinsa ta ba wa matasa ƴan jam'iyyar APC da dama mukamai na siyasa a jihar.
Tun farko jagoran deleget na APC, Muhammad Dan-Sadi, ya shaida wa gwamnan cewa sun ziyarce shi domin nuna godiyarsu bisa dimbin ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ta yi a cikin kankanin lokaci.
“Tabbas mun zabi dan takarar da ba zai ba mu kunya ba,” in ji Dan-Sadi.
Babu sansanin ƴan bindiga a Kebbi
Kun ji cewa Gwamna Nasir Idirs ya bayyana cewa babu sansanin ƴan bindiga ko ɗaya a faɗin jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin ƙasar nan.
Bayan wata ganawa da shugabannin tsaro, Gwamnan ya ce duk ƴan bindigar da ke aikata ta'addanci a jihar daga makotan jihohi suke shigowa.
Asali: Legit.ng