Ana Jimamin Fashewar Tanka, Bakuwar Cuta Ta Bulla a Jihar Neja

Ana Jimamin Fashewar Tanka, Bakuwar Cuta Ta Bulla a Jihar Neja

  • Wata baƙuwar cuta ta ɓulla a garin Bida na jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya na tarayyar Najeriya
  • Cutar wacce ta sanya mutane cikin fargaba da firgici, ta jawo an kwantar da mutane da dama a asibiti bayan sun kamu da ita
  • Kwamishinan lafiya na jihar, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya yi ƙarin haske kan cutar da ƙoƙarin da hukumomi suka yi wajenn kula da masu ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - An samu ɓarkewar wata baƙuwar cuta a garin Bida, hedkwatar hukumar Bida a jihar Neja.

Aƙalla mutane 24 ne mazauna garin Bida aka kwantar a a asibiti sakamakon ɓarkewar baƙuwar cutar.

Bakuwar cuta ta bulla a Neja
An samu bullar bakuwar cuta a Neja Hoto: @HonBago
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an sallami mutum 20 daga cikin waɗanda abin ya shafa bayan sun shafe sama da mako guda a cibiyar lafiya ta tarayya da kuma babban asibitin Umaru Sanda Ndayako da ke Bida.

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya alamun cutar suke?

Cutar wacce aka ce tana sanya mutane sumewa tare da rashin iya yin magana, ta haifar da fargaba a garin.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa adadin mutanen da suka kamu da cutar tun a ranar Litinin ya zarce mutum 20.

Wani mazaunin garin mai suna Abdulmalik Umar ya bayyana cewa wasu ƴan uwansa guda biyu na daga cikin waɗanda abin ya shafa, amma an yi musu magani sannan aka sallame su bayan shafe mako guda suna jinya a asibiti.

"Akwai tsoro sosai a tsakanin al’umma. Mutane suna suma ba zato ba tsammani. Wasu za su kwanta lafiya amma suna farkawa cikin mawuyacin hali ko kasa magana. Abin yana da ban tsoro."
"Wasu waɗanda abin ya shafa suna kasa yin magana, yayin da wasu ke sumewa. Asibitoci har yanzu ba su tantance cutar ba, amma ana kula da marasa lafiya da magungunan zazzabin cizon sauro da taifot."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

- Abdulmalik Umar

Wata majiya da ta buƙaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa cutar tana yaɗuwa cikin sauri, inda kawo yanzu kusan mutane 50 suka kamu da ita.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Da aka tuntuɓi kwamishinan lafiya na jihar Neja, Dakta Bello Tukur, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne sakamakon taifot da zazzabin cizon sauro da ba a kula da su ba.

Ya fayyace cewa babu wani majiyyaci da aka tura wajen Bida, inda ya ce dukkaninsu sun samu kulawa a cibiyar kula da lafiya ta tarayya, babban asibitin Umaru Sanda Ndayako, da kuma cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Laruta, duk a garin Bida.

Gwamnan Neja ya ba gwamnoni shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya ba takwarorinsa na jihohin Arewa shawara kan hanyar bunƙasa ɓangaren ilmi a jihohinsu.

Gwamna Bago ya shawarci gwamnonin da su mayar da harshen Hausa ya zama yaren da za a riƙa koyarwa da shi a dukkanin makarantun yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel