Shaida Ya Cire Tsoro a Kotu, Ya Faɗi Yadda Ministan Buhari Ya Tura Masa Sama da N22bn
- Babbar kotun tarayya ta fara sauraron shaidu a shari'ar tsohon ministan makamashi, Saleh Mamman wanda ake tuhuma da karkatar da N33.8bn
- EFCC ta gabatar da wani ɗan canji a zaman ranar Laraba, wanda ya yi bayanin yadda tsohon ministan ya tura masa N22bn a asusun kamfanoninsa
- Ɗam canjin ya ce ba lokaci guda aka tura kuɗin ba, an daddatsa su kashi-kashi sannan aka tura masa su domin ya ba da Dalolin Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar da yaki da rashawa watau EFCC ta fara gabatar da shaidu a shari'ar tsohon ministan makamashi, Saleh Mamman.
A wannan karon EFCC ta gabatar da wani ɗan canji, Abdullahi Suleiman kuma ya shaidawa kotu yadda tsohon ministan ya tura masa sama da Naira biliyan 22 a asusu.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Asali: Facebook
Yadda ministan Buhari ya canza N22bn zuwa Daloli
A rahoton Daily Trust, Abdullahi Suleman, ya ce Saleh Mamman ya tura masa sama da N22bn a lokuta daban-daban domin ya canza su zuwa dalolin Amurka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mamman na fuskantar tuhume-tuhume 12 da suka shafi hada kai wajen yin safarar kuɗi har na kusan Naira biliyan 33.8 a gwamnatin Muhammadu Buhari.
A zaman kotun na ranar Laraba, lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN), shi ya jagoranci gabatar da shaidar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Shaidar ya bayyana cewa kusan asusunsa 12 na kasuwanci sun karɓi kuɗi daga ma’aikatar makamashi ba tare da yin wani aiki, kwangila, ko aikin da aka tsara ba.
Ma'aikatar makamashi ta tura masa kudi
A wata sanarwa daga kakakin EFCC, Dele Oyewole, kamfanonin da aka ambata sun haɗa da: Prymint Investment Limited, Strong Field International Projects Limited, Mintedge Nigeria Limited da sauransu.
Sai kuma kamfanin ɗan uwansa mai suna Gurupche Business Enterprises da aka yi amfani da su wajen yin mu’amalar kuɗi da tsohon ministan.
Abdullahi Suleiman ya ce wani Alhaji Maina Goje, wanda shi ma abokin kasuwancinsu ne na canjin dala, shi ne ya sa shi a wannan aikin.
Shaida ya yi bayani dalla-dalla a kotu
Shaidar ci gaba da bayani cewa:
“Na kuma san wani Mustapha Muhammad, Goje ya gaya mini cewa shi ne ogansa. Ban san shi ba sai da Maina Goje ya haɗa mu, daga nan ne na fahimci yana aiki da ma’aikatar gidaje."
"Kuma ya umurce ni dacewa idan ya neme shi bai same shi ba, na ba shi duk adadin Dalolin da yake buƙata.”
Lokacin da aka nuna masa kundin shaidun X (Exhibit X), wanda ya ƙunshi bayanan asusun bankunan kamfanonin, shaidar ya tabbatar da cewa waɗannan sune asusun da ya ba Maina Goje.
Bayan sauraron wannan bayanai, Alƙali James Omotosho ya ɗage cigaban shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Janairu.
EFCC: Kotu ta yi fatali da buƙatar Emefiele
A wani rahoton, an ji cewa kotu ta yi fatali da buƙatar tsohon gwamnan CBN, Godwim Emefiele a shari'ar da hukumar EFCC ta gurfanar da shi.
Sai dai kotun ta soke wasu daga cikin tuhume-tuhumen da hukumar EFCC ta gabatar kam Emefiele.
Asali: Legit.ng