Jami'an NDLEA Sun Yi Jarfa da Masu Safarar Kwayoyi a Kano
- Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) sun fuskanci turjiya a yunƙurin cafke wasu da a ke zargi a Kano
- Daga bayan mutanen biyu sun shigo hannu amma ɗaya daga cikinsu ya raunata jami'in hukumar NDLEA a yayin samamen
- Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar ya bayyana cewa da zarar an kammala bincike za a miƙa su zuwa gaban kuliya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), reshen jihar Kano, ta cafke mutane biyu da ake zargi da ta'ammali da kayan.
Hukumar NDLEA ta cafke mutanen masu suna Musa Usman mai shekara 25 da Buhari Ya’u Bashir mai shekara 24, yayin wani samame na musamman a kwanar Rahama, da ke ƙaramar hukumar Bebeji.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

Asali: Facebook
Tashar Channels tv ta rahoto cewa jami'an na NDLEA sun kai samamen ne a ranar, 20 ga watan Janairu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu laifi sun farmaki jami'an NDLEA
A yayin samamen an ba hammata iska tsakanin jami'an NDLEA da waɗanda ake zargi bayan an bankaɗo haramtattun ƙwayoyi da makamai.
NDLEA ta bayyana cewa samamen ya kai ga ƙwace tabar wiwi mai nauyin 1.1kg, ƙwayoyi 38 na diazepam masu nauyin 8gm, da ƙwayoyi 165 na Exol masu nauyin 59gm.
Kwamandan hukumar NDLEA a jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad, ya tabbatar da kama mutanen biyu tare da yin Allah wadai da ƙoƙarin kisan jami'in hukumar da suka yi.
Abubakar Idris Ahmad ya bayyana cewa jami'in da ya samu rauni sakamakon harin yana samun kulawa a asibiti, yayin da ya ba da tabbacin cewa hukumar ba za yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyukanta.
“Lokacin samamen, ɗaya daga cikin wadanda ake zargi, Musa Usman, wanda yake ɗauke da ɗan bida, ya yi ƙoƙarin kai wa jami’anmu hari, wanda hakan ya jawo jikkata ɗaya daga cikin su."
“Harin da ake kai wa jami’an yayin gudanar da aikinsu ba zai hana mu ci gaba da ayyukanmu na kawar da mummunar ɗabi'ar ta'ammali da miyagun kwayoyi da fataucinsu daga cikin al’umma ba."
- Abubakar Idris Ahmad
Mutanen guda biyu da ake zargi na tsare a hannun hukumar, kuma za a gurfanar da su gaban kuliya kan laifukan da suka shafi safarar miyagun ƙwayoyi da kuma kai hari kan jami’in tsaro.
NDLEA za ta kai mutanen gaban kotu
Jami’in hulda da jama’a na hukumar NDLEA reshen jihar Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ya tabbatarwa da Legit Hausa cafke mutanen.
Ya bayyana cewa jami'an hukumar da ke shiyyar Kiru suka cafke mutanen a Bebeji bayan sun yi yunƙurin gujewa a kama su.
"Usman Musa ya yi amfani da ɗan bida wajen sokar jami'inmu, hakan ba abin da haifa masa face dana sani domin hakan bai hana mu kama shi, da shi da kayansa ba."
- Sadiq Muhammad Maigatari
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike yayin da za a miƙa su gaban kuliya nan ba da daɗewa ba.
NDLEA ta cafke mai safarar hodar iblis
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta samu nasarar cafke wanu ɗan kasuwa mai shigo da hodar iblis.
Jami'an na hukumar NDLEA sun cafke ɗan kasuwan ne mai suna Ezeokoli Sylva a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke birnin Legas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng