Gwamnatin Jigawa Ta Kawo Tsarin Ilmi Kyauta har Zuwa PhD, Ta Fadi Wadanda Za Su Amfana

Gwamnatin Jigawa Ta Kawo Tsarin Ilmi Kyauta har Zuwa PhD, Ta Fadi Wadanda Za Su Amfana

  • Gwamnatin jihar Jigawa ta ɗauki hanyar tabbatar da cewa mata sun samu damar yin karatu ba tare da wani tarnaƙi ba
  • An ɓullo da tsarin ba mata ƴan asalin jihar damar yin karatu kyauta har zuwa matakin digirin digirgir watau PhD
  • Shirin zai taimaka wajen ganin mata sun samu damar karatu ko da kuwa ba su fito daga gidajen masu hannu da shuni ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi ta fito da tsarin ba mata damar yin karatu kyauta.

Gwamnatin Jigawa ta fito tsarin ilimi kyauta ga mata ƴan asalin jihar tun daga matakin firamare har zuwa digirin digirgir (PhD) a makarantun gwamnati.

Mata za su yi ilmi kyauta a Jigawa
Gwamnatin Jigawa za ta ba mata damar yin karatu kyauta Hoto: @uanamadi
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta rahoto cewa kwamishinan ilmi mai zurfi na jihar Jigawa, Farfesa Isa Chamo, ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun cafke mai safarar makamai daga Nijar zuwa Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Jigawa za ta ba mata ilmi kyauta

Wannan tsarin na musamman, wanda Gwamna Umar Namadi ke jagoranta, yana da nufin ƙarfafa mata ta hanyar ilimi ba tare da la’akari da fannin karatun da suka zaɓa ba.

Kwamishinan ya bayyana cewa shirin zai yi tasiri sosai a rayuwar ɗalibai mata, rahoton Daily Post ya tabbatar.

"Mun yi imanin cewa wannan shiri zai yi tasiri mai ɗorewa ga rayuwar ɗalibanmu mata. Wannan wani gagarumin mataki ne wajen tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata tare da ƙarfafa mata ta hanyar ilimi."
"Ta hanyar samar da ilimi kyauta ga mata ƴan asalin jiha, gwamnatin Jigawa tana ba wa mata damar kula da rayuwarsu, yanke shawarwari masu kyau da kuma bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban al’ummominsu."

- Farfesa Isa Chamo

Kwamishinan ya bayyana fatan gwamnati na cewa wannan tsari zai jawo hankalin yara mata da yawa su ci gaba da neman ilimi, tare da tabbatar da cewa rashin kuɗi ba zai zama cikas ga burinsu ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

A cewarsa, gwamnatin na fatan ganin cewa duk wata ƴar asalin jihar tana da damar samun ilimi mai kyau wanda zai ba ta damar zama wani abu a rayuwa.

Gwamnati ta yi ƙoƙari kafin fito da tsarin

A nasa ɓangaren, shugaban hukumar ba da tallafin karatu ta jihar Jigawa, Alhaji Sa’idu Magaji, ya bayyana cewa shirin ya samu ne sakamakon jajircewa da aiki tuƙuru.

"Hukumar ta yi aiki tuƙuru don tabbatar da nasarar aiwatar da wannan shiri. Mun yi imanin cewa ilimi shi ne mabuɗin gano baiwar da ɗalibanmu mata suke da ita, kuma za mu ci gaba da tallafa musu a kowane mataki."

- Alhaji Sa'idu Magaji

Wannan tsari na gwamnatin jihar Jigawa ya jawo yabo daga al’ummomi da dama, inda ake ganin zai taimaka wajen kawar da jahilci, da kuma haɓaka cigaban al’umma.

Bisa kawo wannan tsari, gwamnatin Jigawa ta kafa tubalin samun kyakkyawar makoma ga mata ta hanyar tabbatar da cewa babu wata ƴar asalin jihar da za ta rasa damar samun ilimi saboda rashin kuɗi.

Gwamnan Jigawa ya gayyato kamfanin Sin

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya gayyato wani kamfanin ƙasar China domin bunƙasa harkar noma.

Kara karanta wannan

Mazauna Jigawa za su fara ganawa da gwamnansu kai tsaye

Gwamna Umar Namadi ya rattaɓa hannu da kamfanin China CMC Engineering da hukumar kula da noma ta ƙasa (NADF) domin farfaɗo da harkar noma a Jigawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng