Mahdi Shehu Ya Shiga Matsala a Hannun DSS, An Maka Shi a Kotu kan Zargin Ta'addanci

Mahdi Shehu Ya Shiga Matsala a Hannun DSS, An Maka Shi a Kotu kan Zargin Ta'addanci

  • Hukumar DSS ta gurfanar da ɗan gwagwarmayar nan, Mahdi Shehu a gaban kotu a jihar Kaduna kan tuhume-tuhumen da suka shafi ta'addanci
  • A makon da ya gabata ne jami'an tsaron farin kaya suka je har asibitin Mahdi Shehu, suka tafi da shi a karo na biyu
  • Fitaccen mai sharhi kan harkokin siyasar ya fara shiga matsala ne bayan ya saki wani bidiyo da ya zargi gwamnati da ba da izinin kafa sansanin sojin Faransa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Hukumar tsaro ta farin kaya watau DSS ta maka Mahdi Shehu a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Kaduna.

Hukumar DSS ta gabatar da tuhume-tuhumen ta'addanci kan fitaccen ɗan gwagwarmaya wanda ya shahara wajen yi wa gwamnati tonon silili.

Mahdi Shehu.
Hukumar DSS ta maka Mahdi Shehu a Kotu kan tuhumar ta'addanci Hoto: @shehumahdi
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa DSS ta gabatar da tuhume-tuhumen a kotu ne a ranar Juma’a, 17 ga Janairu, 2025, yayin da cikakkun bayanai suka fito a daren Talata.

Kara karanta wannan

Abubuwan da 'yan Najeriya suka fada bayan Buhari ya yi kyautar daloli

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahdi Shehu ya fara fuskantar matsala

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan jami'an DSS sun sake cafke Mahdi Shehu a asibitinsa da ke Unguwar Dosa a cikin birnin Kaduna.

Ɗan gwagwarmayar ya fara fuskantar matsala ne tun bayan sakin wani bidiyo, inda ya yi ikirarin gwamnatin tarayya ta ba sojojin Faransa izinin kafa sansani.

A ranar da ta shigar da ƙarar Mahdi Shehu, DSS ta kuma gabatar da roko na musamman ga kotu, inda ta nemi izinin tsare shi na tsawon kwanaki 60.

Kotu ta ba da umarnin tsare Mahdi Shehu

Hukumar tsaron ta bukaci ci gaba da tsare Mahdi ne bisa tanadin sashe na 66 na Dokar Hana Ta’addanci ta 2022, The Nation ta kawo.

Mai shari’a Rilwan Aikawa na babbar kotun tarayya da ke Kaduna ya amince da rokon, ya ba DSS damar ci gaba da tsare Mahdi Shehu domin kammala bincike.

Laifuffukan ta'addanci da ake tuhumar Mahdi

Kara karanta wannan

Su waye ke daukar nauyin ta'addanci? Hafsan tsaro ya fayyace gaskiya kan lamarin

Laifuffukan da suka shafi ta'addanci da DSS ke tuuhumar Mahdi Shehu sun haɗa da;

1. Wallafa karya domin tayar da hankalin jama’a wanda ya saba wa sashe na 59(1) na dokar laifuffuka ta Tarayya.

2. Yaɗa bayanai na ƙarya kan ayyukan ta’addanci, wanda ya saba wa sashe na 26(2)(a) da (b) na dokar hana ta’addanci ta 2022.

3. Yaɗa bayanin ƙarya da gangan: Wanda ya saba da sashe na 24(1)(b) na dokar laifukan intanet, 2024 da aka yi wa garambawul.

4. Zargin cin amanar ƙasa na karya, wanda ya saba da sashe na 41 na dokar laifuffuka ta Tarayya.

5. Amfani da kafafen sadarwar zamani wajen goyon bayan zargin ƙarya da ke barazana ga tsaron ƙasa, wanda ya saba da sashe na 24(1)(b) na dokar laifukan Intanet.

Tuhume-tuhumen sun samo asali ne daga bidiyon da Mahdi Shehu ya saki kwanakin baya inda ya yi ikirarin cewa gwamnatin Najeriya ta ba Faransa izinin kafa sansanin soji a arewa.

Kara karanta wannan

Shaida ya cire tsoro a kotu, ya faɗi yadda ministan Buhari ya tura masa sama da N22bn

DSS ta kama ɗan gwagwarmaya a Kaduna

A wani rahoton kun ji cewa dakarun DSS sun damke Zubair Zubair, wani ɗan gwagwarmaya a jihar Kano a Arewa maso Yamma.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan kama Zubair, jami'an DSS sun miƙa shi ga ƴan sanda a babban birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262