Bankin Duniya Ya Hukunta Wasu Kamfanonin Najeriya 2, An Gano Dalili
- Bankin Duniya ya kawo shirin tallafawa talakawa da marasa ƙarfi a Najeriya domin su samu sauƙin rayuwa
- Wasu kamfanoni guda biyu na Najeriya da shugabansu sun saka zama da cin hanci a wajen samun kwangilar aikin
- Bankin na duniya ya ɗauki matakin dakatar da su daga shiga duk wani shiri ko aiki da yake ɗaukar nauyi har na tsawon watanni 30
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Bankin Duniya ya ɗauki matakin ladabtarwa kan kamfanoni biyu na Najeriya, Viva Atlantic Limited da Technology House Limited, tare da shugabansu Mista Norman Didam.
Bankin na duniya ya dakatar da kamfanonin na watanni 30 saboda aikata zamba da cin hanci da rashawa dangane da aikin taimakon marasa galihu a Najeriya.

Source: Getty Images
Bankin Duniya ya samu kamfanonin Najeriya da laifi
Jaridar The Punch ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Bankin Duniya ya fitar a ranar Litinin.
Bankin ya bayyana cewa aikin, wanda aka tsara don samar da tallafin kuɗi ga talakawa da marasa ƙarfi, ya samu cikas sakamakon ayyukan rashin gaskiya da aka gudanar a lokacin sayen kayan aiki a shekarar 2018.
"Bankin Duniya na sanar da dakatar kamfanoni biyu da ke Najeriya, Viva Atlantic Limited da Technology House Limited tare da shugabansu, Mista Norman Bwuruk Didam."
"Dakatarwar na da nasaba da zamba, haɗa baki da cin hanci da rashawa a aikin taimakon marasa galihu a Najeriya."
- Bankin Duniya
Meyasa aka dakatar da kamfanonin?
Bankin Duniya ya bayyana cewa Viva Atlantic Limited, Technology House Limited, da Norman Didam sun yi rashin gaskiya a kwangilar, sannan sun samu bayanai na sirri game da kwangilar daga jami’an gwamnati.
Sanarwar ta ƙara da cewa abin da suka yi, ya saɓawa dokar hana cin hanci da rashawa ta Bankin Duniya.
Haka kuma, bankin ya ce Viva Atlantic Limited da Didam sun ƙirƙiri ƙarya kan tarihin ƙwarewar kamfanin, sun miƙa takardun iznin ƙera kayan bogi, kuma sun ba jami’ai wasu kyaututtuka, wanda aka ɗauki hakan a matsayin cin hanci da rashawa.
Waɗannan laifukan, a cewar bankin, sun lalata gaskiyar shirin ba da tallafin da aka tsara don taimakawa mutane mafi rauni a cikin al’ummar Najeriya.
Me dakatarwar bankin duniya ke nufi?
Dakatarwar ta hana kamfanonin biyu da Norman Didam shiga cikin duk wani aiki ko shirin da Bankin Duniya ke ɗaukar nauyi har na tsawon lokacin da aka ƙayyade.
A wani ɓangare na yarjejeniyar sulhu, waɗanda abin ya shafa sun amince da laifinsu, kuma sun yi alƙawarin cika wasu sharuɗɗa, ciki har da ɗaukar matakan gyara.
Tinubu ya ci bashi daga Bankin Duniya
A wani labarin kuma, kun.ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ts ci bashi daga wajen Bankin duniya.
Gwamnatin ta ciyo bashin na $1.7bn daga Bankin Duniya ne domin gudanar da wasu muhimman ayyuka a Najeriya.
Ayyyukan da za a gudanar da kuɗaɗen da aka ci bashin za su shafi ɓangaren ilmi, noma da harkar lafiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

