Niger: An Kara Samun Gawarwaki Sanadin Fashewar Tanka, Ana Ci Gaba da Aikin Ceto
- Yawan mutane da suka mutu a gobara daga fashewar tankar fetur a Dikko da ke jihar Niger sai karuwa yake yi
- Aƙalla a yanzu mutane da suka mutu sun kai 86, yayin da 55 suka jikkata, an kuma yi jana’izar gama-gari
- Gwamnan Niger, Mohammed Umar Bago, ya hana ababen hawa daga hanyar Maje amfani da gadar Dikko, yana mai nuna takaici
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Minna, Niger - Adadin mutanen da suka mutu sakamakon fashewar tankar fetur a Dikko, jihar Niger sai kara gaba yake yi.
A yanzu rahotanni sun tabbatar da cewa mutane 86 suka mutu yayin da wasu 55 suka jikkata a ranar Asabar 18 ga watan Janairun 2025.

Asali: Original
Yawan mutane da suka mutu sun karu
A jiya Asabar, rahotanni sun nuna cewa mutane 70 sun mutu, sannan 50 sun samu raunuka, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma daga baya, an gano karin gawarwaki, kuma duka an yi musu jana’izar gama-gari a Dikko da ke jihar Neja.
Daraktan Hukumar ba da agaji a jihar, Abdullahi Baba-Arah, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi 19 ga watan Janairun 2025.
Ya ce hukumar, tare da karamar hukumar Gurara da masu bayar da agaji, sun gudanar da jana’izar gama-gari daga karfe 5 na yamma zuwa tsakar dare.
“Mutane 86 ne aka tabbatar sun mutu, kuma an gano gawarwakinsu tare da yi musu jana’iza."
“An binne 80 a rami guda a harabar cibiyar kiwon lafiya ta Dikko, yayin da iyalan wasu biyar suka dauki gawarsu, daya kuma ya mutu a cibiyar."
“Hukumar NSEMA tare da karamar hukumar Gurara da masu bayar da agaji ne suka gudanar da wannan aiki daga karfe 5 na yamma zuwa tsakar dare."
- Abdullahi Baba-Arah.
Hakan ya biyo bayan hatsarin tankar fetur a ranar Asabar da safe a kwanan Dikko, dake tsakanin jihohin Niger da Kaduna.
Yayin da wasu mazauna yankin ke kokarin deban fetur da ya zubo daga tankar a kan hanya, sai tankar ta kama wuta, ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Gwamna Bago ya ziyarci wurin Iftila'in
Gwamnan Jihar Niger, Mohammed Umar Bago, ya kai ziyara wurin wannan mummunan hadari ranar Asabar, ya kuma hana ababen hawa daga Maje amfani da gadar Dikko.
Sakataren watsa labaran gwamnan, Bologi Ibrahim, ya tabbatar da wannan umarni a wata sanarwa ranar Lahadi.
“Gwamnatin jihar Niger ta umarci a dakatar da duk wata mota daga Maje daga amfani da gadar Dikko."
“Gwamna Mohammed Umaru Bago ya bayar da wannan umarni lokacin da ya kai ziyara wurin fashewar tankar a kwanan Dikko.
“Ya kuma roki kwamandan FRSC ya kafa sansani a yankin don tabbatar da bin umarnin, tare da kiran dukkan kungiyoyin sufuri da su bada hadin kai."
- Cewar sanarwar
An rasa rayuka a Niger sanadin fashewar tanka
Kun ji cewa Aƙalla mutane 30 ake fargabar sun mutu, ciki har da wata mata mai juna biyu sakamakon fashewar tankar mai a Dikko Junction a jihar Neja.
A farko tankar ta zubar da mai, lamarin da ya ja mutane suka taru don diban man fetur, wanda daga bisani mummunan gobara ta tashi a wurin.
Asali: Legit.ng