Jami'an EFCC Sun Faɗa Tarkon da ba Su Yi Tsammani ba, An Yi Masu Ruwan Wuta
- Wani jami’in hukumar EFCC ya rasa ransa sa'ilin da wasu ƴan damfara ta yanar gizo, Yahoo Boys, suka bude musu wuta a jihar Anambra
- Haka nan kuma wani jami’i a tawagar dakarun EFCC ya samu mummunan rauni kuma yana cikin mawuyacin hali a asibiti da ba a bayyana ba
- Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da cewa ta kama wanda ake zargi da kuma kwato makamin, sannan ta ci gaba da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Anambra - Wasu ‘yan damfara ta yanar gizo waɗanda aka fi sani da ƴan Yahoo Boys sun buɗewa jami'an EFCC wuta a jihar Anambra.
Ƴan damfarar waɗanda aka gani ɗauke da mugayen makamai sun far wa jami'an hukumar yaƙi da masu yu wa tattalin arziki ta'adi watau EFCC ba zato ba tsamnani.

Asali: Twitter
Yan damfara sun hallaka jami'in EFCC
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ƴan Yahoo sun bindige jami'i ɗaya na EFCC har lahira a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin, wanda ya faru a ranar Juma’a, 17 ga watan Janairu, 2025 ya jikkata wani jami’i EFCC guda ɗaya.
Sauran dakarun hukumar EFCC kuma sun yi kokarin guduwa domin tsira daga harbe-harben da ake masu ba tare da sun yi tsammani ba.
Jami'an hukumar EFCC ta faɗa tarko a Anambra
An ce jami’an sun fito ne da nufin zuwa kamo wata kungiyar da ake zargin ƴan damfara ta yanar gizo, da aka fi sani da Yahoo Boys ne, ba zato suka faɗa wannan tarkon.
Jami’i ɗaya na EFCC da ya rasu a farmakin ya kai matssyin mataimakin sufurtanda a hukumar mai yaki da cin hanci da rashawa.
Haka kuma an tattaro cewa ya kammala wata jarabawar karin matsayi kwanan nan kafin faruwar lamarin wanda ya zama ajalinsa a jihar Anambra.
Har zuwa daren Juma’a, jami’in da ya jikkata a harin yana cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Ƴan sanda sun fara bincike kan harin
Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa sun fara bincike don gano haƙiƙanin abin da ya faru.
“Yanzu haka muna kan bincike kan wannan al’amari mai tayar da hankali. Mun kama wanda ake zargin kuma an kwato bindigar, za mu fitar da karin bayani nan gaba,” in ji Ikenga.
Hukumar EFCC ta tsare jami'anta guda 10
A wani labarin, kun ji cewa hukumar yaƙi da masu karɓar rashawa ta ƙasa watau EFCC ta cafke wasu jami'anta bisa zargin yin sama da faɗi da wasu kayayyakinta.
Shugaban EFCC na ƙasa ne ya ba da umarnin cafkewa tare da tsare jami'an su 10 da ke aiki a ofishin Legas har sai an kammala bincike kan zargin da ake masu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng