Mutuwa Ta Ratsa Filin Kwallo, Allah Ya Yi wa Wani Ɗan Wasa Rasuwa a Wasan Karshe

Mutuwa Ta Ratsa Filin Kwallo, Allah Ya Yi wa Wani Ɗan Wasa Rasuwa a Wasan Karshe

  • Wani lamari mai ban tausayi ya faru yayin wasan karshe na gasar tunawa da Isiaka Adeleke, yayan Gwamna Adeleke a ranar Alhamis
  • Ɗan wasan kwallon kafa mai shekaru 29, Adeyemi Adewale, ya rasa ransa yayin da kungiyarsa ke buga wasan ƙarshe a jihar Osun
  • Lamarin ya ɗaga hankulan magoya baya da masu shirya gasar, musamman saboda ya faru a ranar da ɗan wasan ya cika shekaru 29 da haihuwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Al'ummar jihar Osun sun shiga cikin alhini da jimami yayin wasan ƙarshe na gasar cin kofin tunawa da marigayi Isiaka Adeleke karo na biyar.

Wani matashin ɗan kwallon, Adeyemi Adewale, ɗan shekara 29 ya rasu yana tsaka da taka leda a wasan ƙarshe na kofin tunawa da ɗan uwan Gwamna Ademola Adeleke.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta

Jihar Osun
Wani matashin dan wasan kwallo ya rasu ana tsskiyar buga wasan ƙarshen a jihar Osun Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu, 2025 a filin wasa da ke makarantar kimiyya ta Ataoja, inda aka shirya gasar, kamar yadda The Nation ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan kwallo ya mutu ana tsaka da wasa

An shirya gasar cin kofin ne domin tunawa da yayan Gwamna Adeleke, Isiaka Adeleke karo na biyar.

Rahotanni sun bayyana cewa Adewale, wanda ke wakiltar kungiyar kwallon kafa ta Ilesa ta Yamma, ya yanke jiki ya fadi ne a lokacin wasansu da kungiyar Ejigbo.

Bayanai sun nuna cewa wasan shi ne na ƙarshe a gasar cin kofin ya zo daidai da ranar da ɗan kwallon ke bikin cika shekara 29 a duniya.

Wannan ya kara girman baƙin cikin mutuwarsa, wanda ya bar manyan tambayoyi da alhini cikin zukatan abokan wasa da magoya baya.

Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce matashin ya cika ne bayan an isa asibiti.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Kakakin ƴan sandan ta ce:

"Ya yanke jiki ya fadi ne a cikin fili kuma nan take aka garzaya da shi zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Osun (UNIOSUNTH), inda aka tabbatar da cewa Allah ya masa rasuwa daga baya."

Gasar kwallon kara da aka saba shiryawa duk shekara domin tunawa da gudunmawar marigayi Isiaka Adeleke ya bayar a jihar, wannan karon ta zo da abin alhini.

Magoya bayan sun fara jimamin wannan rashi

Tuni dai magoya baya da masu shirya gasar suka shiga cikin jimami, suna jajanta wannan rashin mai ban tausayi.

An tabbatar da cewa yanzu haka an kai gawarsa dakin ajiye gawa na asibitin don gudanar da bincike, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rasuwar Adewale ta bar babban gibi a gasar, inda magoya baya ke ci gaba da alhini game da wannan mummunan lamari.

Wannan ya zama gargaɗi ga masu shirya wasanni da al’umma gaba ɗaya wajen tabbatar da tsaro da lafiyar ‘yan wasa a kowanne lokaci.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun kashe farfesan jami'a a gidansa

Ƴan fanshi sun farmaki ƴan wasan kwallo

A wani rahoton, an ji cewa wasu tsagerun ƴan fashi sun farmaki tawagar ƴan wasan ƙungiyar El-Kanemi Warriors a titin Jos zuws Bauchi.

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta ce dakarunta sun bazama domin kamo maharan da suka aikata wannan laifin su fuskanci hukunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel