Lokaci Ya Yi: Tinubu Ya Yi Alhinin Rasuwar Babban Kusa a APC
- Jam'iyyar APC ta yi rashi na ɗaya daga cikin manyan jigoginta a jihar Legas da ke yankin Kudu maso Yamma na Najeriya
- Pa Akinsanya Sunny Ajose wanda ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ma'aikatan jihar a lokacin Bola Tinubu, ya yi bankwana da duniya
- Shugaban ƙasa ya aika da saƙon ta'aziyyarsa ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu, gwamnatin jihar Legas da iyalan marigayin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Wani jigo a jam’iyyar APC kuma na kusa da Shugaba Bola Tinubu, Pa Akinsanya Sunny Ajose, ya rasu.
Pa Akinsanya Sunny Ajose, wanda ya wakilci Badagry a majalisar dattawan APC ta Legas (GAC), ya rasu ne da safiyar ranar Alhamis, 16 ga watan Janairun 2025.
Jaridar Tribune ta rahoto cewa ɗan majalisar dokokin jihar Legas mai wakiltar Badagry, Hon. Solomon Bonu Saanu, ne ya sanar da rasuwarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya yi alhinin rasuwar jigon APC
Shugaban kasa, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X, ya jajantawa al’ummar Badagry kan rasuwar wannan dattijo.
Ya bayyana marigayi Sunny Ajose a matsayin dattijon kirki, mai kishin jam’iyya, wanda ya taka muhimmiyar rawa a jihar Legas.
Shugaba Tinubu ya tuna alaƙarsa da Ajose a lokacin da ya kasance shugaban ma’aikatan jihar lokacin da yake gwamna, inda ya ce marigayin ya jajirce wajen gyaran ma’aikatan Legas.
“Ya kasance ƙwararren mai gudanarwa kuma gogaggen ma’aikacin gwamnati. Lokacin da na naɗa shi shugaban ma’aikata, ya zama babban jigo."
"Ya samu babban tasiri a kan ma’aikata. Ya taka muhimmiyar rawa wajen sanya ma’aikata su goyi bayan manufofinmu da tsare-tsarenmu."
"Ko bayan wa’adinsa a matsayin shugaban ma’aikata, mun ci gaba da kasancewa tare saboda ƙwarewarsa wajen jagoranci da rawar da yake takawa wajen cigaban jihar."
- Shugaba Bola Tinubu
Tinubu ya ce Sunny Ajose ya bayar da gagarumar gudunmuwa wajen ci gaban jihar Legas ba yankin Badagry kawai ba.
Yayin da yake jajantawa Gwamna Babajide Sanwo-Olu, gwamnati da al’ummar jihar, Shugaba Tinubu ya yi addu'ar Allah ya ba iyalan marigayin haƙurin jure wannan rashin.
Wanene Pa Akinsanya Sunny Ajose?
An haifi Ajose a ranar 10 ga Fabrairu, 1946, a Badagry. Bayan kammala karatunsa na firamare da sakandare a Najeriya, ya tafi Amurka don karatun digiri.
Ya samu kwalin digiri daga jami'ar Illinois da ke birnin Chicago na ƙasar Amurka a shekarar 1973.
Marigayi Sunny Ajose ya yi digirinsa na biyu a jami'ar Governors da ke Amurka a sheƙarar 1974.
Ya fara aiki da gwamnatin jihar Legas a shekarar 1979 sannnan ya zama shugaban ma'aikatan jihar a shekarar 2004.
Olusegun Obasanjo ya ba Bola Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ba mai girma Bola Ahmed Tinubu shawara kan ilmi.
Olusegun Obasanjo ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ba da fifiko wajen samar da wadatattun kuɗi ga ɓangaren ilmi domin samun ci gaba mai ɗorewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng