Gwamna Zulum Ya Gargadi Jama'a bayan 'Yan Ta'adda Sun Kashe Manoma a Borno
- Gwamnan jihar Borno ya kai ziyara a yankin Baga bayan ƴan ta'addan Boko Haram sun hallaka manoma 40 kwanan nan
- Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi gargaɗi ga mutanen yankin kan haɗa kai da ƴan ta'adda, ya ce hakan barazana ce ga tsaro
- Ya buƙaci manoman da ke yankin Baga da kewaye da su riƙa gudanar da ayyukansu a wuraren da sojoji suka amince a riƙa shiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya gargadi mutanen ƙauyukan da ke noma da kiwo a Baga da su guji haɗa kai da ƴan ta’addan Boko Haram.
Gwamna Zulum ya bayyana irin wannan haɗa kan a matsayin babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Gwamna Zulum ya yi wannan gargaɗin ne yayin da yake jawabi ga jama'a a fadar hakimin yankin Baga a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zulum ya yi gargaɗi kan haɗa kai da ƴan ta'adda
Zulum ya yi Allah wadai da duk wani nau’in haɗa kai da ƴan ta’adda, inda ya bayyana hakan a matsayin abin ƙyama kuma barazana ga ƙoƙarin dawo da kwanciyar hankali a jihar.
Ya buƙaci mutanen yankin da su riƙa yin nomansu a wuraren da sojoji suka sahale a riƙa shiga, rahoton Channels tv ya tabbatar.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin da sojojin Najeriya da kuma gwamnatin jihar Borno suka gindaya.
“Ina kira ga mutanen Baga da kewaye su gudanar da ayyukan nomansu ne kawai a wuraren da sojoji suka amince da su."
"Duk da cewa muna maraba da ayyukan noma, yana da matuƙar muhimmanci mutanenmu su bi ƙa’idojin don tabbatar da tsaronsu da kuma kwanciyar hankali a jihar."
- Farfesa Babagana Umara Zulum
Gwamna Zulum ya yabawa sojoji
Ziyarar gwamnan ta biyo bayan wani hari ne da ƙungiyar ƴan ta'addan ISWAP ta kai kwanan nan a Dumba, cikin Karamar hukumar Kukawa ta jihar.
Harin da ƴan ta'addan suka kai kan ƴan ta'addan ya yi sanadiyyar mutuwar manoma 40.
Gwamnan, wanda ya samu kyakkyawar tarba a garin Kukawa, ya yi alƙawarin hanzarta ayyukan sake gina ɓangarorin ilimi, kiwon lafiya da kayan more rayuwa.
Haka kuma, ya yabawa sojojin bataliya ta 101 ta bisa jarumtar da suka nuna, inda ya tabbatar musu da ci gaba da samun goyon baya daga gwamnatin jihar.
Gwamna Zulum ya samu rakiyar ƴan majalisar tarayya da manyan jami’an gwamnati a yayin ziyarar da ya kai yankin.
Gwamna Zulum ya ba ɗa tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya halarci taron jami'an sojoji na rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) a ƙasar Chadi.
Gwamna Zulum ya ba da tallafin N300m ga iyalan jami'an sojojin da suka rasa rayukansu a faɗan da suke yi da ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng