Gwamna Bala Ya Fadi Dalilin Yin Zazzaga a Gwamnatinsa, Ya Yi Sabon Albishir

Gwamna Bala Ya Fadi Dalilin Yin Zazzaga a Gwamnatinsa, Ya Yi Sabon Albishir

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya taɓo batun korar da ya yi wa wasu daga cikin kwamishinonin da ke gwamnatinsa
  • Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa ya sallami kwamishinonin ne ba don rashin gaskiya ko ƙwarewa a wajen aiki ba
  • Gwamnan ya kuma rantsar da sababbin kwamishinoni guda takwas, ya buƙaci su yi gaskiya wajen sauke nauyin da aka ɗaura musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana dalilin da ya sanya ya kori wasu daga cikin kwamishinoni a gwamnatinsa.

Gwamna Bala ya ce sauyin da ya yi a majalisar zartarwarsa, wanda ya haifar da cire wasu kwamishinoni guda biyar, an yi shi ne domin saka kowa a matsayinsa da ya dace da shi.

Bala Mohammed ya rantsar da sababbin kwamishinoni
Gwamna Bala ya rantsar da sababbin kwamishinoni a gwamnatinsa Hoto: Sen Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake rantsar da sababbin kwamishinoni guda takwas da ya naɗa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

"Ku maida Hausa yaren koyarwa a makarantu," Gwamna ya ba gwamnonin Arewa shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Gwamna Bala ya kori kwamishinoni?

Sanata Bala Mohammed ya tabbatar da cewa bai kori kwamishinonin da abin ya shafa saboda wata matsala ta rashin gaskiya ko ƙwarewa ba.

Ya ƙara da cewa, duk da cire su daga majalisar zartarwa, akwai yiwuwar a basu muƙaman masu ba da shawara na musamman a nan gaba.

Gwamna Bala ya rantsar da sababbin kwamishinoni

Gwamna Bala ya jaddada cewa an zaɓo sababbin kwamishinonin ne bisa cancanta, ƙwarewa, da kuma tabbatar da adalci wajen wakilci.

Ya yi kira ga sababbin kwamishinonin da su yi amfani da dukiyar gwamnati yadda ya kamata, tare da gujewa karkatar da kuɗaɗen jama'a zuwa amfanin kansu.

Ya bayyana cewa an rantsar da kwamishinoni takwas, maimakon guda biyar da aka cire, saboda bukatar maye gurbin wasu manyan muƙamai biyu, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Ya ce an maye gurbin tsohon kwamishinan tsare-tsare da tattalin arziƙi, Hon. Aminu Hammayo da na marigayi Aliyu Ahmed Jalam, wanda ya riƙe muƙamin kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masaarautu kafin rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Abba ya yabi jami'i mai amana, kwamitin rabon kayan makaranta ya maido rarar N100m

Sababbin kwamishinonin da aka naɗa a Bauchi

Sababbin kwamishinonin da muƙamansu sun haɗa da, Alhaji Usman Usman Shehu (watsa labarai da sadarwa), Dr. Iliyasu Aliyu Gital (noma), Dr. Bala Musa Lukshi (ci gaban dabbobi), Hon. Isa Babayo Tilde (ƙananan hukumomi da masarautu).

Sauran su ne Farfesa Titus Saul Ketkukah (ayyuka da sufuri), Alhaji Adamu Babayo Gabarin (matasa da wasanni), Alhaji Abdullahi Mohammed (filaye da safiyo) da Dr. Lawal Mohammed Rimin Zayam (ilmi).

Gwamna Bala ya ba da sababbin muƙamai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya dawo da wasu daga cikin kwamishinonin da ya kora zuwa cikin gwamnati.

Bala ya ɗauko uku daga cikin kwamishinonin guda biyar da ya sallama, ya ba su muƙaman masu ba da shawara na musamman.

Gwamnan ya yi kira a gare su da su yi amfani da ƙwarewar da suke da ita wajen ba da gudunmawar da ta dace a ƙoƙarin da yake yi na kawo ci gaba a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Ana raɗe raɗin zai koma APC, gwamna ya kori kwamishina daga aiki

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng